Malaman Kano sun ba wa mutanen Bormo tallafin kayan miliyan N410

Malaman Musulunci a Jihar Kano sun bayar da gudummawar kaya na Naira miliyan 410 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Jihar Borno

Malaman Kano sun ba wa mutanen Bormo tallafin kayan miliyan N410

Wani sashe na gidajen ‘yan majalisar Kogi da ruwa ya mamaye

Gamayyar Malaman Musulunci a Jihar Kano ta bayar da gudummawar kaya na Naira miliyan 410 ga mutanen da ambaliya ta shafa a Jihar Borno.

Wakilan kungiyar malaman, wanda Farfesa Muhammad Babangida ya jagoranta domin ziyarar jaje ga Gwamna Babagana Zulum a Maiduguri, ya ce gudummawar kayan na da muhimmanci idan aka yi la’akari da girman bukatun mutanen da ambaliyar ta shafa.

Farfesa uhammad Babangida, ya bayyana cewa, “girman ɓarnar da ambaliyar ta yi ya wuce duk yadda mutum ke tunani.

“Haƙiƙa al’ummar sun yi fama da matsaloli daban-daban, kama daga rikicin Boko Haram zuwa gobara zuwa ambaliyar ruwa.

“Ba don Allah Ya taimake su kyakkyawan jagoranci na wannan gwamna ba, da wataƙila halin da al’ummar za su shiga a sakamakon wannan ibtila’i sai ya fi haka muni.

“Dom haka nake kira a gare ka da kada ka daina kyawawan ayyukan da kake yi.”

Da take mayar da jawabi, Zulum ya mika godiyarsa ga malaman bisa tallafin kayan da suka bayar da kuma ziyarar da suka kai domin jajanta wa al’ummar Borno bisa wannan ibtila’i.