Malaman Kenya sun yi maraba da karin albashi

A ranar Litinin da ta gabata ne Kotun kolin Kenya ta umarci gwamnatin kasar ta kara wa malaman makaran albashi kashi 50 cikin 100 na kudin da ake biyansu.Ita dai gwamnatin ta sha cewa ba za ta iya biyan malaman kusan 200,000 karin albashi ba.Sai dai bayan malaman sun gurfanar da gwamnati a gaban kotun, […]

Malaman Kenya sun yi maraba da karin albashi
Malaman Kenya sun yi maraba da karin albashi

A ranar Litinin da ta gabata ne Kotun kolin Kenya ta umarci gwamnatin kasar ta kara wa malaman makaran albashi kashi 50 cikin 100 na kudin da ake biyansu.
Ita dai gwamnatin ta sha cewa ba za ta iya biyan malaman kusan 200,000 karin albashi ba.
Sai dai bayan malaman sun gurfanar da gwamnati a gaban kotun, sun yi nasarar samun karin albashin.
Malaman sun yi barazanar tafiya yajin aiki idan ba a kara musu albashin ba.
Sun ce albashin da ake ba su ba ya isar su, domin kuwa wasun su suna daukar abin da bai wuce $100 (kimanin naira dubu 19).
An dai kwashe shekara 18 ana takaddama tsakanin malaman da gwamnati kan karin albashin. An fara kulla yarjejeniyar ne a shekarar 1997, amma sai gwamnati ta ki mutunta tanade-tanaden da ta kunsa gaba daya.
Wakilin BBC a birnin Nairobi ya ce malaman sun farin cikinsu da hukuncin kotun, inda ma fi kankantar malami zai karbi Dala 240 (kimanin naira dubu 47 ke nan)