Malaman Kwalejin Kimiyya ta Kaduna na shirin shiga yaji

Malaman Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna sun yi barazanar shiga yajin aiki matukar mahukuntan kwalejin ba su magance wasu matsalolinsu ba. Shugaban kungiyar Malaman Kwalejin Injiniya Musa Ibrahim ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.Injiniya Musa Ibrahim ya ce akwai matsalolin da suke addabar kwalejin da suka shafi malamai da […]

Malaman Kwalejin Kimiyya ta Kaduna na shirin shiga yaji
Malaman Kwalejin Kimiyya ta Kaduna na shirin shiga yaji

Malaman Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna sun yi barazanar shiga yajin aiki matukar mahukuntan kwalejin ba su magance wasu matsalolinsu ba.

Shugaban kungiyar Malaman Kwalejin Injiniya Musa Ibrahim ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
Injiniya Musa Ibrahim ya ce akwai matsalolin da suke addabar kwalejin da suka shafi malamai da kuma ci gaban makarantar. “Mun yi zama da shugabannin kwalejin amma ba mu samu shawo kan wadannan matsaloli ba. Idan kuwa aka ci gaba da haka wata ran za a zo a tarar da kwalejin ta zama wani abu daban. Wannan ya sa muke rokon shugabannin kwalejin su yi wani abu domin magance matsalolin. Yanzu haka mu malamai mun soma zaman dirshan domin nuna bacin ranmu a kan abubuwan da suke faruwa a makarantar.
Ma’ana malami zai shiga aji amma ba zai koyar da dalibai darasi ba, kuma za mu yi haka ne na tsawon kwana uku,” inji shi.
Ya ce idan ba a warware matsalar ba za su shiga yajin aiki na kwana uku a makon gobe. “Shi yajin aikin ba sonsa muke yi ba saboda haka za mu sake zama nan da kwana uku domin kauce wa shiga yajin aikin kai-tsaye saboda tausaya wa dalibanmu. Muna sane da cewa da zarar an tafi yajin aiki dalibai ke cutawa amma kuma mene ne amfanin dalibai idan ba a karantar da su abubuwan da suka kamata? Wannan ya sa muke matsa wa hukumar makaranta ta magance matsalolin,” inji shi.
Ya ce bukatunsu kashi biyu ne, da suka hada da matsalar rashin karin girma ga malamai, inda tun shekarar 2011 suke bin kudin karin girma har kashi uku. Sai kuma batun alawus da suke bi da aka dakatar da shi a watan Fabrairu, wanda kafin mahukuntan kwalejin su dakatar da shi suna bin na wata 36 da a ba biya su ba.
Injiniya Ibrahim ya ce akwai kuma matsaloli da dama da suka shafi makarantar, musamman rashin kafar sadarwa ta intanet a makarantar mai malamai sama da dubu daya ba ta da yanan gizo da malamai za su rika amfani da shi domin yin bincike.
Ya ce babu wuta a makarantar duk da manyan janaratoci da ke a kwalejin amma sanya musu dizel ya zama matsala. Sannan sai dalibai sun shiga asibitin dantsaho da Asuba debo ruwan da za su yi amfani da shi, ga rashin wuraren bahaya da sauran matsalolin da suke ganin ba su fi karfin hukumar kwalejin ta magance su ba.
Sai ya nemi Gwamnatin Tarayya ta waiwayi batun mayar da kwalejin Jami’ar Kimiyya da Fasaha da aka bayyana tun a shekarar 2006. Ya ce kwalejin ta cancanci zama jami’a ba ma daya ba tana iya zama jami’o’i hudu, saboda tana da tsangayoyi hudu da babu wacce ba ta fi wata jami’a girma a kasar nan ba. “Ba mu san dalilin tsayar da wannan tafiya ba, amma tunda aka samu wannan sabuwar gwamnatin wanda muke ganin ta zo gyara ne shi ya sa muke mika kukanmu cewa mun cancanci zama jami’a,” inji shi.
Injiniya Ibrahim ya ce suna da kwararrun malamai masu digirin digirgir sama da 90 da ke koyarwa a yanzu. Ya ce idan aka zagaya wasu jami’o’in ba su da masu irin wadannan takardu fiye da 30 ko 40.