Malaman Kwalejojin Ilimi sun yanke shawarar ci gaba da yajin aiki

kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi na Tarayya (ASUP) ta yanke shawarar ci gaba yajin aikin da ta fara kusan wata shida da suka gabata, har sai Gwamnatin Tarayya ta biya su dukkan hakkokinsu.Shugaban kungiyar na Kwalejin Ilimi ta Tarayya FCE (T) da ke Gombe Mista danladi Aliyu Msheliza, ya bayyana haka a wani taron manema labarai […]

Malaman Kwalejojin Ilimi sun yanke shawarar ci gaba da yajin aiki
Malaman Kwalejojin Ilimi sun yanke shawarar ci gaba da yajin aiki

kungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi na Tarayya (ASUP) ta yanke shawarar ci gaba yajin aikin da ta fara kusan wata shida da suka gabata, har sai Gwamnatin Tarayya ta biya su dukkan hakkokinsu.
Shugaban kungiyar na Kwalejin Ilimi ta Tarayya FCE (T) da ke Gombe Mista danladi Aliyu Msheliza, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da suka kira a Gombe bayan sun tattauna matsalolin da suka shafe su.
Mista Danladi Msheliza, ya ce kungiyarsu ta shiga yarjejeniya da gwamnatin kimanin shekara biyar da suka gabata inda ta zayyana mata matsalolin da suke so a biya musu amma har yanzu shiru, shi ya sa a wannan karon suka ce ba za su janye wannan yajin aikin ba har sai an ji kukansu.
“Ba a son ranmu ne ’ya’yan talakawa ke gida ba maimakon makaranta ba, mun yi haka ne saboda mu ma muna da bukatun da muke son a biya mana da muka gaya wa gwamnati tun a shekarar 2009 kafin mu janye yajin aikin,” inji Msheliza.
Ya ce sun yi ta rubuta takardun koke da na tuni ga Shugaban kasa da Ministan Ilimi amma har yanzu gwamnati ba ta waiwaiye su ba. Ya ce cikin dalilansu na shiga yajin aikin akwai rashin ba da isassun kudi don gudanar da harkokin makarantu da samar da wadatattun ababen zama ga dalibai. Sai kuma kudin karin girma na ma’aikata da tsohon Shugaban kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa ya sanya wa hannu a shekarar 2010 inda duk ma’aikaci daga mataki na daya zuwa na 15 za a kara masa girma da mataki daya, sai ga shi an yi na wadanda suke kan mataki na daya zuwa na 12 sauran ba a yi musu ba har yanzu.
Shugaban ya ce sun yi kokarin kauce wa shiga yajin aiki amma ganin gwamnati ta ki sauraronsu ya sa suka shiga yajin.