Malaman Musulunci na duniya sun yi Allah-wadai da fim din Iran da ya tozarta Manzon Allah (saw)
Manyan malaman Musulunci na duniya sun nuna takaicinsu tare da yin Allah wadai da wani sabon fim da aka shirya a kasar Iran kan tarihin rayuwar Manzon Allah Muhammad (SAW), mai suna “Muhammad Messenger of God” wanda kuma aka haska shi a birnin Montreal na kasar Canada a yayin bikin nuna fina-finai na duniya da […]
Manyan malaman Musulunci na duniya sun nuna takaicinsu tare da yin Allah wadai da wani sabon fim da aka shirya a kasar Iran kan tarihin rayuwar Manzon Allah Muhammad (SAW), mai suna “Muhammad Messenger of God” wanda kuma aka haska shi a birnin Montreal na kasar Canada a yayin bikin nuna fina-finai na duniya da aka gabatar ranar 27 ga Agustan da ya gabata. Haka kuma an nuna fim din a gidajen silima sama da 140 a sassa daban-daban na kasar Iran.
Kamar yadda aka tsara fim din mai tsawon minti 171, an nuno wani jariri cikin tsumman goyo, aka kamanta shi da haihuwar Manzon Allah (SAW), sannan a wurare da dama an nuno shi bayan ya girma, yana kiwon dabbobi da sauran harkokin rayuwa kamar yadda tarihinsa ya nuna.
Fim din dai na hadin gwiwa ne tsakanin kamfanonin Noor-eTaban na kasar Iran da kuma Infinite Production Company na kasar Jamus. Haka kuma Muhammad Mehdi Heidarian ne ya shirya shi, a yayin da Majid Majid ya kasance wanda ya bayar da umarni.
Babban malamin Musulunci na duniya na farko da ya tofa albarkacin bakinsa dangane da fim din shi ne, Sheikh Abdul Aziz Al-Asheikh, Babban Mufti na kasar Saudiyya, wanda ya yi Allah-wadai da fim din da cewa Musulunci bai yarda a zayyana surar Manzon Allah (SAW) kamar yadda aka yi a fim din ba.
Ya ce fim din ya kaskantar da darajar Manzon Allah (SAW) sannan ya wofintar da gagarumin sakon da ya kawo ga duniya. “Wannan shashanci ne aka nuna wa Manzon Allah (SAW) kuma an kaskantar da darajarsa,” inji shi.
Su ma manyan malaman Musulunci da ke Jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar, sun yi Allah wadai da fim din a makon jiya, inda kuma suka bukaci Gwamnatin Iran ta haramta fitar da shi ga al’umma.
Abdul Fatah Al-Awari, Shugaban Tsangayar Ilimin Tauhidi ta Jami’ar Al-Azhar ya ce: “Haramun ne a shari’ar Musulunci a siffanta wani da surar annabawa.”
Ita ma Gamayyar Kungiyar Musulmi ta Duniya Rabita (The Muslim World League) ta shiga cikin sahun al’ummar Musulmin da suka yi Allah wadai da sabon fim din. Kamar yadda Sakataren kungiyar, Abdullah bin Abdulmohsen Al-Turki ya bayyana wa jaridar ‘The Arab News,’ ya ce kwata-kwata bai dace ba kuma bai kamata a nuna hotunan wani mutum a siffanta shi da Manzon Allah (SAW), fiyayyen halitta a cikin fim, kamar yadda aka yi ba.
“Ina kira ga hukumomin Tehran su yi gaugawar dakatar da nunawa da fitar da wannan fim, sannan kuma ina kira ga daukacin Musulmin duniya su kaurace wa kallon fim din,” inji Al-Turki.
Fim din, wanda aka ruwaito cewa an kashe kimanin Dala miliyan 40 (kimanin Naira biliyan takwas) wajen shirya shi, shi ne fim mafi tsada da aka taba shiryawa a tarihin shirya fina-finai a kasar Iran.
A nasa bangaren, daraktan da ya ba da umurni a fim din, Majid Majid, ya ce sun shirya fim din ne da nufin bunkasa hadin kan al’ummar Musulmi. Ya ce kudurin aikin shirya fim din, wanda kashi uku ne, shi ne domin dawo da martabar Musulunci, saboda kuwa a cewarsa, masu wuce gona da iri sun gurbata martabarsa.
Masu lura da al’amuran yau da kullum sun yi mamakin yadda aka shirya wannan fim a kasar Iran, ganin cewa a bara kasar ta yi Allah wadai da mujallar ‘Charlie Hebdo’ ta kasar Faransa, wacce ta fitar da zanen hotunan batanci ga Manzon Allah, Muhammad (SAW), sai ga shi a yau kuma an shirya fim a kasarta, wanda Musulmin duniya suka yi ittifakin bai dace ba, kasancewar ana nuna wani mutum a matsayinsa.