Malaman Musulunci sun yunkuro don shawo kan mace-macen mata da kananan yara

Tsawon shekaru ana ta bullo da dabarun shawo kan yawan mace-macen kananan yara da mata masu juna biyu, duk da cewa manuniyar kididdiga ta nuna an samu ragowar mace-mace, amma dai akwai bukatar a kara kaimi. Don haka Cibiyar bincike tad RPC, ta bullo da sabuwar hanyar ceton rayuka da aka yi wa lakabi da […]

Malaman Musulunci sun yunkuro don shawo kan mace-macen mata da kananan yara
Malaman Musulunci sun yunkuro don shawo kan mace-macen mata da kananan yara

Tsawon shekaru ana ta bullo da dabarun shawo kan yawan mace-macen kananan yara da mata masu juna biyu, duk da cewa manuniyar kididdiga ta nuna an samu ragowar mace-mace, amma dai akwai bukatar a kara kaimi. Don haka Cibiyar bincike tad RPC, ta bullo da sabuwar hanyar ceton rayuka da aka yi wa lakabi da ‘ceton rayuka a lokacin haihuwa,’ inda ta samu talalfin kungiyar GCC, a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2013, don gudanar da ayyukanta a fadin jihohin Katsina da Jigawa, wato jihohin da ke yankin arewa maso Yammacin Najeriya.
Tsare-tsaren ayyukan cibiyar sun ta’allaka ne wajen bayar da kariya ga mata masu sabuwar haihuwa, tare da kula da lafiyar jariransu, ta hanyar kulla alaka malaman addini da shugabannin al’umma a jihohin Katsina da Jigawa.
dasya daga cikin malaman da suka taru a otal din Tahir don yin bita kan sasbuwar hanyar bincike, Dokta Iliyasu, ya bayyana muhimmancin malaman addini, tare da irin tasirinsu wajen warware matsalolin da suka addabi al’umma, ta hanyar wa’azi da ayyukansu a aikace. Sannan ya kara da cewa malamai na warware matsalolin iyali da zamantakewar al’umma da tabbbatar da adalci da yada ilimi da inganta harkokin kasuwanci da kula da harkokin lafiya.
Shi ma wani malamin jami’a, Dokta Musa Muhammad Bello na tsangayar koyon Likitancin kula da lafiyar al’umma, da ke Jami’ar Bayero ta Kano, ya yi nuni d amatsayin malaman addini, musamman ganin yadda Musulunci ya karade kowane bagire na rayuwa, don haka ya bai wa malamai fifiko. “Bisa la’akari da muhimmancinsu, shi yasa aka zabo malamai biyar daga kowace karamar Hukuma da ke cikin jihohuin da aka zaba,” inji shi.