Malaman ‘Poly’ sun janye yajin aiki
Malaman kwalejin kimiyya da kare-kere sun janye yajin aikin da suka ta tsundumna na mako biyu. Kungiyar malaman kwalejojin ta ASUP ta bukace su da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, 2022. Bashir Ahmad: Hadimin Buhari ya fadi zaben fitar da dan takara ’Yan bindiga sun kashe ango sun sace […]
Malaman kwalejin kimiyya da kare-kere sun janye yajin aikin da suka ta tsundumna na mako biyu.
Kungiyar malaman kwalejojin ta ASUP ta bukace su da su koma bakin aiki daga ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, 2022.
- Bashir Ahmad: Hadimin Buhari ya fadi zaben fitar da dan takara
- ’Yan bindiga sun kashe ango sun sace amarya da iyalan kwamishina a Kaduna
Da yake sanar da janye yajin aikin, kakakin ASUP, Abdullahi Yalwa, ya ce sun yanke shawarar janye yajin aikin ne a taron Kwamitin Zartarwar kungiyar, inda suka tattauna ka bukatun kungiyar da ya sa suka shiga yajin aikin.
A cewarsa, gwamnati ta biya hudu daga cikin bukatunsu tara da suka gabatar mata, shi ya sa skue ganin dacewar janye yajin aikin.
A cewarsa, za su dakatar da yajin aikin ne domin ba wa gwamnatin tama da kuma lokacin yin abin da ya dace game da ragowawr bukatun malaman kwalejojin.