Malaman sakandare sun yi zanga-zanga kan rashin biyansu albashi na wata takwas
daruruwan malaman makarantun sakandaren a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu albashi na wata takwas.Malaman sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne sakamakon fusata da suka yi game da kalaman da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano wanda kuma har ila yau shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Hafizu Abubakar ya yi […]
daruruwan malaman makarantun sakandaren a Jihar Kano sun gudanar da zanga-zanga kan rashin biyansu albashi na wata takwas.
Malaman sun bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne sakamakon fusata da suka yi game da kalaman da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano wanda kuma har ila yau shi ne Kwamishinan Ilimi na Jihar, Farfesa Hafizu Abubakar ya yi a lokacin wata hira da wani gidan rediyo inda ya ce babu ma’aikatan da ke bin gwamnati bashin albashi.
Malaman sun zargi gwamnatin Jihar Kano da nuna halin ko-in-kula ga matsalar tasu inda suka ce sun sha kai wa gwamnatin kuka, amma har yanzu ba ta biya musu bukatarsu ba.
Da yake magana a madadin malaman, Malam Sadik Sabitu ya ce an dauke su aiki ne a shekarar 2013 a matsayin ma’aikatan wuncin-gadi inda a watan Janairun bana aka mayar da su ma’aikata na dindindin, sai dai tun da aka ba su takardar daukar aiki ta dindindin ba su sake karbar albashi ba.
Malam Sabitu ya ce a lokuta da dama sun sha bibiyar gwamnati don sanin makomarsu, sai dai amsar da suke samu a kullum ita ce su kara hakuri gwamnati na sane da su.
“Ko a kwanakin baya mun kai kukanmu fadar Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II daga wannan lokaci ne a farkon watan jiya aka kira mu aka tantance mu aka kuma ba mu lambar da za mu karbi albashi da ita, amma har yanzu ba mu ji sako ba,” inji shi.
Malam Sabitu ya ce kalaman Mataimakin Gwamna ba karamin jefa rayuwarsu cikin matsala suka yi ba, inda wasu da dama zama a gidajensu ya gagare su sakamakon masu neman biyan bashi da suke yi musu tururuwa suna neman su biya su bashin kudin da suka karba a wurinsu.