Malaman Sunni sun ce daular ISIL haramtacciya ce

Fitattun malamai da kungiyoyin Musulunci da suka fito daga bangarorin Sunni sun yi fatali da da’awar kungiyar kasar Musulunci (ISIL) ta kafa Daula ko Khilafar Musulunci. Malaman da kungiyoyin sun bayyana da’awar kafa daular da haramtacciya kuma ta kauce wa hanya ce a daidai lokacin da mayakan kungiyar ke ci gaba da samun suka daga malamai […]

Malaman Sunni sun ce daular ISIL haramtacciya ce
Malaman Sunni sun ce daular ISIL haramtacciya ce

Fitattun malamai da kungiyoyin Musulunci da suka fito daga bangarorin Sunni sun yi fatali da da’awar kungiyar kasar Musulunci (ISIL) ta kafa Daula ko Khilafar Musulunci.
 Malaman da kungiyoyin sun bayyana da’awar kafa daular da haramtacciya kuma ta kauce wa hanya ce a daidai lokacin da mayakan kungiyar ke ci gaba da samun suka daga malamai da wasu kungiyoyi da suke da alaka da Alka’ida da suka samo asali daga gare ta.
Gidan talabijin na Aljazeera wanda ya ruwaito haka a shafinsa na intanet, ya ruwaito Assem Barkawi, wanda aka fi sani da Abu Mohammed al-Makdesi, da aka sako shi daga kurkukun kasar Jordan a watan Yuni kan laifin daukar sojojin sa-kai zuwa yaki a Afghanistan yana kiran mayakan da ke biyayya ga shugaban ISIL Abubakar al-Baghdadi da “karkatattu.”
Makdesi wanda mai goyon bayan kungiyar Nusra Front mai alaka da Alka’ida ne, ya soki kungiyar ISIL kan tsauraran hanyoyin da take bi. “Shin wannan khilafa kariya ce da zama mafaka ga raunanan Musulmi, ko kuwa wani takobi ne a wuyan duk Musulmin da ya saba mata?,” inji Makdesi.
Wannan fatali da da’awar kafa khilafar da Makdesi ya yi wanda Basalafe ne ya sa ra’ayinsa ya zo daidai da na wasu shugabannin Sufaye kamar Muhammad al-Yacoubi na kasar Siriya da ke gudun hijira wanda a shafinsa na tiwita ya bayyana magoya bayan ISIL da “karkatattu.” “Da’awar kafa khilafar haramtacciya ce, kuma goyon bayanta haram ne,” inji Yacoubi.
Shi kuwa fitaccen malamin nan na Masar da ke zaune a katar Sheikh Yusuf kardawi wanda ya bayyana da’awar kafa daular da haramatacciya a bisa dokokin Musulunci ya ce: “Da’awar wata kungiya ta kafa khilafanci bai isa ya samar da khilafanci ba,” kamar yadda ya fadi a wata budaddiyar wasika da aka buga a shafin intanet na kungiyar Malaman Musulunci ta Duniya (International Union of Muslim Scholars) da yake shugabanta.
kungiyoyin da suka soki kafa khilafar sun hada da wata jam’iyyar Musulunci mai suna Hizb ut-Tahrir, mai da’awa kafa khilafancin Musulunci wadda ta ce batun kafa khilafa ba karamin lamari ne da wani zai jirkita shi don biyan bukatunsa ba. Ita ma Jam’iyyar Ennahada ta Rachid Ghannouchi da ke Tunisiya ta ce kafa khilafar ‘shakiyanci ne’ da ke isar da mugun sako ga duniya. Ta ce ba a kafa kasa ta irin wannan rashin kan gado.