Malamar jinya ta yi ta bakin aikinta bayan lalata da marar lafiya a Birtaniya
A yanzu an dakatar da ita na wata 18, a matsayin matakin farko.
Wata malamar jinyar masu larurar ƙwaƙwalwa ta yi ta bakin aikinta bayan lalata da wani majinyaci a yankin Shropshire da ke Birtaniya.
Matar da aka kora daga aiki mai suna Samantha Bourton wadda ke aiki da gidauniyar ma’aikatar lafiya ta Birtaniya, an gano cewa tana zuwa gidan majinyacin har a lokutan da ba na aiki ba.
Wani kwamitin bincike da aka kafa ya kuma gano cewa ta ƙi bayar da rahoton cewa mara lafiyan ya taɓa yin tunanin kashe kansa.
Hukumar tantance malaman jinya da ungozoma ta Birtaniya ta ce ba za a lamunci wannan ɗabi’a ta malamar jinyar ba, la’akari da cewa ƙimar aikin zai zube idan aka bar ta ta ci gaba da aiki.
A cikin wani bayani, kwamitin ya ce Ms Bourton ba ta musanta cewa ta sadu da majinyacin ba a watan Mayu na 2021.
Kwamitin ya ce ta tuntuɓi mutumin ta hanyar amfani da lambar waya ta ƙashin kanta sannan ta ziyarce shi sau biyu a lokutan da ba na aiki ba.
Sai dai an gano cewa sauran ziyarar da ta kai masa daga baya, ba ta yi ne domin yin lalata da shi ba.
A yanzu an dakatar da ita na wata 18, a matsayin matakin farko, inda za ta iya ɗaukaka ƙara a tsakanin wa’adin.
Sai dai idan ba ta ɗaukaka ƙara ba, korar ta tabbata.