Malami ya bai wa dalibansa nasarar jarabawa saboda murnar baiko

  Wani malami a Saudiyya ya shiga rudani bayan da dauki alkawarin cewa daukacin dalibansa za su ci jarabawa saboda murnar baikonsa. Malamin ya yi alkawarin samar da nasarar jarrabawa 100 bissa 100 kamar yadda ya rubuta wa dalibai a takardar tambayoyin jarrabawarsu. “Saboda bikin baikona, babu dalibin da zai fadi. daukacin dalibai za su ci […]

Malami ya bai wa dalibansa nasarar jarabawa saboda murnar baiko
Malami ya bai wa dalibansa nasarar jarabawa saboda murnar baiko

  Wani malami a Saudiyya ya shiga rudani bayan da dauki alkawarin cewa daukacin dalibansa za su ci jarabawa saboda murnar baikonsa.

Malamin ya yi alkawarin samar da nasarar jarrabawa 100 bissa 100 kamar yadda ya rubuta wa dalibai a takardar tambayoyin jarrabawarsu.

“Saboda bikin baikona, babu dalibin da zai fadi. daukacin dalibai za su ci jarrrabawa,” a cewar malamin kamar yadda aka rubuta a takardun tambayoyin jarrabawa, wadda jaridar Al Madina ta ruwaito.

Mafi yawan masu tsokaci a sshafukan zumuntar intanet sun harzuka har sun soki lamirrin malamin.

“dabi’arrsa ba ta dace ba, kuma ba ta kamata ya bayar da tabbacin samun ansara a kan takardar jarrrabawa ba,” a cewar Mohammad Al harbi, wani da ya aike da ra’ayinsa zuwa shafin sadarwar Al Madina.

Om Touta, wani mai amfani da kafar sadarwar, cewa ya yi, wannan rashin tunani ne, domin makomar dalibai nan gaba ta dogara ne kan yanayin yadda malaminsu ya kasance.

Ita kuwa Sahar cewa ta yi, wannan abin takaici ne da keta haddin dalibai masu kwazo, wadanda “aka daifdaita su da malalata kan cewa duk za su ci.”

Sai dai Al Nayfa cewa ta yi babu wata illa tattare da alwashin malamin. “Mun yaba da cewa malamin yana cike da annnashuwa, don haka yake son dalibansa su yi farin cikin irin nasa. Wannan al’amari daidai ne, babu wata matsala tattare da shi.

Shi kuwa Abrar nuni ya yi da cewa alkawarta samun nasarar da malamin ya yi tabbaci ne da yake da shi. “Yana da tabbacin cewa daukacinsu za su jarabawar, saboda sun samu cikakkken horo,” inji ta.

Lateefa cewa ta yi malamin ya san dalibansa masu jajircewa ne da aiki tukuru, don haka ya yanke cewa za ssu ci jarabawarsu.