Malami ya kara lalata karamar yarinya
An kama wani fasto dan shekara 59 da ya yi wa ’yar shekara 10 fayade a jihar Ogun. Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce faston ya aiki yarinyar dakinsa ne ta kai sako, amma ya bi ta ciki ya lalata ta da karfin tsiya. “A lokacin bincike faston ya amsa cewa ya aikata […]
An kama wani fasto dan shekara 59 da ya yi wa ’yar shekara 10 fayade a jihar Ogun.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce faston ya aiki yarinyar dakinsa ne ta kai sako, amma ya bi ta ciki ya lalata ta da karfin tsiya.
“A lokacin bincike faston ya amsa cewa ya aikata laifin kuna ana ci gaba da tsare shi a caji ofis na Odeda, ita kuma yarinyar an kai ta asibiti domin duba lafiyarta”, inji shi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Ogun, Kenneth Ebrimson ya umarci a mika faston ga sashen binciken laifukan safarar mutane da bautar da yara domin ci gaba da bincike kafin gurfanar da shi a kotu.
Karo na biyu ke nan a cikin mako guda ana kama fastoci masu fyade a jihar Ogun.
Fyade daga masu kare yara
Da farko an kama wani fasto da ya yi ta yi wa diyar cikinsa fyade tana daukar ciki yana kai ta ana zubarwa har sau uku.
A baya-bayan nan rahotannin yi wa kananan yara fyade musamman daga mutanen da ya kamata su kare su na yawaita.
A makon jiya, an kama wani jami’in agaji mai kula da kananan yara da ya yi ta lalata wata ‘yar shekara goma a jihar Borno.
Bayan nan kai karar wani fasto mai shekaru 50 da zargin ya yi wa diyar makwabcinsa fyade.
A makonnin bayan an tsinci gawar wata ’yar shekara shida da aka yi wa fyada a wani masallaci a jihar Kaduna.
Gabanin haka an yi wa wata ’yar wata uku fyade a jihar Nasarawa, inda ’yan sanda suka gurfanar da wani matashi da zargin aikata laifin.