Malami ya kashe dalibinsa a Masar

Ana gudanar da bincike a Masar kan mutuwar wani yaro dan shekara 12 sakamakon dukan kawo wuka da daya daga cikin Malamansa ya yi masa, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana. A ranar Alhamis ne aka garzaya da yaron asibiti daga makarantarsa da ke birnin Alkahira domin duba ba shi.Yaron mai suna […]

Malami ya kashe dalibinsa a Masar
Malami ya kashe dalibinsa a Masar

Ana gudanar da bincike a Masar kan mutuwar wani yaro dan shekara 12 sakamakon dukan kawo wuka da daya daga cikin Malamansa ya yi masa, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

A ranar Alhamis ne aka garzaya da yaron asibiti daga makarantarsa da ke birnin Alkahira domin duba ba shi.
Yaron mai suna Islam Sharif, ya rasu ne a ranar Lahadi sakamakon mummunan raunin da ya ji a kansa.
An dai dakatar da malamin da ya yi dukan daga aikinsa, yana dai aikin ne a wata makarantar gwamnati da ke unguwar marasa galihu, kuma ‘yan sanda na gudanar da bincike a kansa. Inda ake tuhumarsa da yin amfani da karfin tuwo wajen dukan yaron, wanda har hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Duk da cewa an haramta azabtarwa, amma har yanzu makarantu a Masar na yi wa yara bulala a matsayin horo.
A watan Disambar bara ne, wata hukuma da ke kula da mata da yara a kasar ta ce azabtar da yara ya karu da kashi 55 cikin 100 tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban shekarar, idan aka kwatanta da shekaru uku da suka wuce. Kuma galibin rahotannin gallazawar suna faruwa ne a makarantu.
Har ila yau, a watan Satumbar baran ne, aka yanke wa daraktan wani gidan marayu da ke birnin Alkahira hukunci duarin shekara uku sakamakon azabtar da yara kanana.