Malami ya kusan gutsure yatsun almajirinsa
Wani almajiri mai suna Abbas danmaliki mai shekara tara a duniya ya kusan rasa yatsunsa na hannu takwas a dalilin hukuncin da malaminsa ya dauka a kansa.Wani mai suna Malam Babangida Gidan Dabalo a Bakin Kasuwa cikin Zariya ya shaida wa wakilinmu cewa wani lokaci Abbas ya taba zuwa gidansu da wani almajiri kamarsa. “Kasancewar […]

Wani almajiri mai suna Abbas danmaliki mai shekara tara a duniya ya kusan rasa yatsunsa na hannu takwas a dalilin hukuncin da malaminsa ya dauka a kansa.
Wani mai suna Malam Babangida Gidan Dabalo a Bakin Kasuwa cikin Zariya ya shaida wa wakilinmu cewa wani lokaci Abbas ya taba zuwa gidansu da wani almajiri kamarsa. “Kasancewar haka ne da ya samu kansa a wannan hali ya yi gudun hijira zuwa gidan namu, inda muka wayi gari ne muka gan shi da safe da wannan rauni a hannunsa biyu,” inji shi. Ya ce da suka tambaye shi sai ya ce malaminsa ne yayi masa hukunci ta hanyar daure masa hannu saboda bai kwana a gida ba.
Malam Babangida ya ce akwai wata ’yar uwarsa mai suna Ummul-Khairi wadda matar aure ce ita ce take daukar dawainiyar Abbas tun zuwansa gidan.
Da wakilinmu ya tuntubi Ummul-Khairi mai shekara 19 ta ce ita take yi wa Abbas wanka da aski da canja masa kaya da ba shi abinci a baki tun zuwansa gidan. Ta kara da cewa, “Na kai shi asibitin marigayi Mustapha Bawa domin a duba shi a nan ne suka karbi kudi a hannunna mai sauki, suka yi masa aiki domin wasu jijiyoyin yatsunsa sun riga sun tsinke. Na ci gaba da kai shi asibitin, sai wata rana wani mai aikin haya da babur ya gan mu ya ce Abbas kane yake a wurinsa, tun daga wannan rana muke zuwa asibiti da yayan na Abbas.”
Ta ce sun je har gidan malamin su Abbas, amma ba su samu ganinsa ba, don an ce ya tafi garinsu.
Abbas ya shaida wa Aminiya cewa daga garin Magami ya fito, babansa ne ya hada shi da Malam Amadu ya ce ya zo da shi Zariya ya yi karatun allo, kuma sun taho Zariya a daminar bana.
Ya ce, “Wata rana mun tafi bara sai ban samu abinci ba, sai na kwana a wani gida a unguwar da muke zaune wato Unguwar Bishar, da safe sai na je makaranta da Malam ya gan ni sai ya sa aka daure ni a hannu aka hada da turmi na kwana a haka da safe aka saka ni a mari. Bayan faruwar haka da Malam ya tafi garinsu sai na gudu aka yanke mini marin shi ne na je wannan gidan da ake mini magani.”
Dokta Bashir Abubakar Magaji, Mataimakin Shugaban Asibitin Marigayi Mustapha Bawa Taimako Clinic, ya shaida wa Aminiya cewa, “An kawo mana yaro mai suna Abbas wanda yatsun hannunsa duka biyu suna cikin rauni matsananci domin kuwa ba ya ga wari da suke yi hatta jijiyoyinsu sun tsinke. Sai da muka yi hikima ta wajen yi masa dinki, gaskiya al’amarin abin tausayi ne, duk da mun saba yi wa masu rauni jinya na wannan yaron daban ne, saboda har kuka wadansu ma’aikatanmu suka yi.”
Wakilinmu ya je gidan malamin a Unguwar Bishar don jin ta bakinsa, amma aka ce ya tafi gida Zamfara domin ya taho da wasu daliban.
Wata majiya ta shaida mana lamarin ya kai gaban masarautan Zazzau, inda Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya dauki nauyin ci gaba da yi wa Abbas magani tare da tabbacin in Allah ya ba shi sauki za a rubuta takarda ga masarautar Zamfara don daukar matakin da ya dace.
Sai ya yaba Ummul-Khairi bisa nuna tausayi da kulawa da Abbas tare da fatan za ta ci gaba da irin wannan aikin alheri, kuma ya nemi al’umma su yi koyi da ita.