Malamin addini a Saudiyya ya raba wa jaruman fim da mawaka mata 100 kyaututtuka
Shahararren malamin addinin Musulunci a kasar Saudiyya, mai suna Muhammad Al Arafi, ya sha yabo da suka, bayan da ya shiga kafafen yada labarai yana raba wa mawaka da jaruman fim mata 100 kyaututtukan littattafai da turare; sannan ya gode musu da suka karbi kyautarsa.Shahararren malamin ya bai wa matan kyautar wani dan akwati da […]
Shahararren malamin addinin Musulunci a kasar Saudiyya, mai suna Muhammad Al Arafi, ya sha yabo da suka, bayan da ya shiga kafafen yada labarai yana raba wa mawaka da jaruman fim mata 100 kyaututtukan littattafai da turare; sannan ya gode musu da suka karbi kyautarsa.
Shahararren malamin ya bai wa matan kyautar wani dan akwati da ke dauke da Alkur’ani, da makalolin da ya gabatar a wa’azozinsa da kwalbar turare, kamar yadda ya bayyana a shafin sadarwarsa na twitter, wanda a kalla mutum miliyan bakwai da dubu 600 ke bibiyarsa.
Jerin wadanda ya raba wa kyaututtukan sun hada da shahararrun matan da ke aiki a kafafen yada labarai, al’amarin da ya jawo masa suka da yabo
“Akwai bukatar malaman addini su yi takatsantsan wajen ma’amala da mata, wadanda ba su rufe kawunansu da lullubi ba,” a cewar daya daga cikin masu sukarsa, sannan ya bijiro da tambaya kan ko me yasa Al Arafi ke hulda da su. Wani kuwa cewa ya yi, “ko me Al-Arafi zai ce idan wani ya bai wa matarsa kyauta?”
Wani mai shafin sadarwa cewa ya yi, “duniya na cike da abubuwan mamaki, ana bai wa mawakiya kyauta, ana yi mata godiya, alhali kananan yara a Siriya na fama da sanyi da yunwa.”
Su kuwa magoya bayan malamin cewa suka yi, “wannan wata sabuwar dabara ce ta ma’amala, wadda aka yi ta da kyakkyawar niyya.”
Mohammad Al Herwan, wani mai shafin sadarwa, cewa ya yi, “Malamin na ba su shawara su karanta Alkur’ani, su kuma saurari karatun wa’azinsa. Sai dai abin takaici, akwai mutanen da kokarin yin batanci ga kyakkyawar niyyarsa, wadanda ke ganin mummunan abu a tare da aikin wannan malamin addini.” Shi ma Al Nawmas, ya bayyana cewa: “Wannan manufa ce mai daraja ta daya,” kuma tana nuni da kyakkyawar niyya.
Jaridar Aminiya ta taba ruwaito muku yadda sheikh Al Arafi ya roki wata shahararriyar mawakiya a Hadaddiyar Daular Larabawa, kan ta daina waka, ta koma wa’azi, cikin azumin bara.