Malamin da ya bayar da fatawar hana mata noma ya shiga hannu
Ana zargin wani malamin addinin Musulunci da bayar da fatawar haramta wa mata aikin gona, lamarin da ya haifar aka kama shi a kasar Bangladesh, kamar yadda ’yan sanda suka bayar da sanarwa a Larabar da ta gabata. Limamin da masu kula da masallaci su biyar na fuskantar tuhumar laifin sanarwar da tta ingiza al’ummar […]
Ana zargin wani malamin addinin Musulunci da bayar da fatawar haramta wa mata aikin gona, lamarin da ya haifar aka kama shi a kasar Bangladesh, kamar yadda ’yan sanda suka bayar da sanarwa a Larabar da ta gabata.
Limamin da masu kula da masallaci su biyar na fuskantar tuhumar laifin sanarwar da tta ingiza al’ummar karkarar yankin Yammacin Kumarkhali suka yi kokarin hana mata zuwa aikin gona.
“Sun yanke wannan matsayar ne bayan da aka kammala sallar juma’a, inda suka haramta wa mata fita daga gidajensu na aure,,” a cewar babban jami’an ’yan sandan karkarar Abdul Khalekue a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.
“Sun yi amfani da amsa kuwwar masallacin wajen baza wannan labarin manufarsu.”
kasar Bangladesh wadda mafi yawan al’ummarta Musulmi ne, tsarin tafiyar da harkokin mulkin al’umma ba ruwansa da addini, amma malaman addini na da matukar tasirin juya akalar tunanin al’umma, musamman a yankunan karkarar kasar, inda jama’a ke zamantakewa da tunani na ra’ayin rikau.
An hana yin fatwa tun a shekarar 2001, amma babbar kotun kasar ta yanke hukuncin cewa za a iya yi kan al’amuran da suka shafi mutuntaka da harkokin addini, matukar ba su tursasa aiwatar da haddi ba.
kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun soki lamirin hukuncin, inda suka ce kauyuka sun yi hannun riga da kotunan Bangladesh wadanda ba ruwansu da addini, don haka ake amfani da fatwa wajen yi musu hukunce-hukuncen da suka saba wa dokokin kasar.
A da mata a karkarar Bangladesh ana tsare su ne a gidajensu, amma saboda karancin ma’aikata, shi ya sa miliyoyinsu ke aiki a gonaki wajen girbin amfani ko lokacin shuka.
Kusan mata ne suka kwashi kaso 80 cikin 100 na ma’aikatan kasar miliyan hudu da ke aiki a masakun kasar 4,500, wuraren da ke tallafar tattalin arzikin kasar mai fama da talauci.
’Yan sanda sun ce mutane shiddan da aka kama za su fuskanci tuhuma a kotunan masu karfin iko na musamman, wato karkashin tsohuwar dokar soja da ake takaddama a kanta.