Malamin da ya sumar da dalibarsa da duka ya shiga tsomomuwa

Wani malami mai suna Mista Sabestine da ake zargin ya doki dalibarsa mai suna Abigail har ta suma kan ta ki bin umarninsa a jihar Legas ya shiga tasku domin iyayenta sun sha alwashin ci gaba da bin hakkin ’yarsu, har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi. A makon da ya gabata […]

Malamin da ya sumar da dalibarsa da duka ya shiga tsomomuwa
Malamin da ya sumar da dalibarsa da duka ya shiga tsomomuwa

Wani malami mai suna Mista Sabestine da ake zargin ya doki dalibarsa mai suna Abigail har ta suma kan ta ki bin umarninsa a jihar Legas ya shiga tasku domin iyayenta sun sha alwashin ci gaba da bin hakkin ’yarsu, har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.
 A makon da ya gabata ne iyayen yarinyar suka zargi Mista Sabestan, malamin kimiyya a makarantar sakandare ta Iponri Estate Senior High School  da ke unguwar Surulere a Legas da yi wa ’yarsu Abigail Chidinma da ke ajin SS1 dukan kawo-wuka har sai da ta fadi sumammiya.
Rahotanni sun nuna cewa an yi ta zuba mata ruwa na tsawon lokaci sannan ta farfado, daga bisani aka sallame ta tafi gida.
Mahaifin yarinyar, Mista Enyenwa, wanda ya ki yarda a dauki hotonsa ko na iyalinsa, ya shaida wa Aminiya cewa malamin ya dade yana cin zarafin yarinyar ba dalili.
Ya ce, “Ya tilasta mata tsuguno da daga hannu, ta yi masa biyayya kuma duk da haka bai kyale ta ba, sai ya kama dukanta har sai da ta suma. Wannan cin zali ne kuma cin zarafin dan Adam. Ni ban ce kada a yi wa ’yata horo ba, amma a san yadda za a yi mata horo ta hanyar da ta dace. Wadansu malaman ma fa sukan yi hakan ne idan yarinyar ta ki ba su hadin kai su neme ta. Saboda haka za mu ci gaba da bin hakkinta, har sai yadda hali ya yi”.
Ita ma Abigail ta yi karin bayani cewa, “Ya fito da mu a gaban a ji wai mun yi surutu. Sai ya ce mu durkusa mu daga hanneyenmu, duk na yi abin da ya ce, amma sai kawai na ji ya rufe ni da duka. Daga nan ban san yadda aka yi ba, sai gani na yi ana zuba mini ruwa. Daga bisani aka kai ni ofishin shugabar makaranta, daga nan kuma na taho gida na shaida wa iyayena yadda aka yi”.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin shugabar makarantar Misis Anyah ya ci tura, amma daga bisani bayan matsin lamba, sai ta ce su ma’aikatan gwamnati ne ba su da damar yin magana da manema labarai.
Mista Sabestine ba ya makarantar a lokacin da Aminiya ta je a safiyar Litinin, amma wata majiya ta shaida mata cewa yana buya ne saboda gidun kada jami’an tsaro su kama shi.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Mis Ngozi Braide ta bayyana cewa har yanzu ba ta sami labarin aukuwar lamarin ba.
dalibai da dama da Aminiya ta tattauna da su, a bayan fage, sun tabbatar da aukuwar lamarin, inda wasu suka tattabar da sun ga lokacin da ’yan sanda suka kama malamin.