Malamin firamare ya rasa ’ya’ya hudu a gobara
Mutanen kauyen Dambo da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna sun hadu da abin jimami na konewar wadansu yara kanana su hudu ’ya’yan mutum daya a wata gobara da ta auku a Alhamis din makon jiya.Maihaifin yaran mai suna Shehu Suleiman Dambo mai kimanin shekara 32 malamin makarantar firamare ne kuma ya bayyana wa […]
Mutanen kauyen Dambo da ke karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna sun hadu da abin jimami na konewar wadansu yara kanana su hudu ’ya’yan mutum daya a wata gobara da ta auku a Alhamis din makon jiya.
Maihaifin yaran mai suna Shehu Suleiman Dambo mai kimanin shekara 32 malamin makarantar firamare ne kuma ya bayyana wa Aminiya cewa, “A ranar Alhamis da misalin karfe 9:00 na dare da barci ya kama ni sai na ce su koma dakunan iyayensu su bar ni in huta, domin sun saba sai sun yi barci a dakina kafin in dauke su in koma da su dakin iyayensu, to da misalin karfe 9:30 sai na ji ihu, ina fitowa sai na ga wuta ta kama a dakin uwargidana, muka rasa ta inda za mu shiga dakin. Da mun tunkari dakin sai wutar ta biyo mu kuma ba ta inda za mu shiga na dauki dagi na fasa dakin ta baya domin in shiga in ceto yaran nan amma ina, duk inda muka bi sai wutar ta biyo mu, muna ji muna gani yaran nan suka kone kurmus.”
Ya ce “Babban cikinsu mai suna Abubakar dan kimanin shekara shida shi ne ya yi kokari ya fito da rarrafe ta kofa amma wutar ta fado a kansa da yake silin din dakin na roba ne haka yake narkewa yana zuba kamar fetur har wutar ta kone yaran nan kurmus muna ji muna gani, kuma a zatonmu wutar ta samo asali ne daga wutar lantarki ,domin ba a dade da kawo ta ba gobarar ta tashi.
Mahaifiyar yaran ta kara wa Aminiya bayani cikin damuwa cewa, “Yarana maza hudu har da na goye duk sun kone babbansu Abubakar mai shekara shida da masu bi masa Hassan da Husaini masu shekara uku-uku da na goye mai suna Izzuddin dan shekara daya yana bayana a goye sai na kwance shi na dawo da shi cikin ’yan uwansa na kwantar da shi da yake shi ma kwanansa ya kare na ta fi dakin daya daga cikin matan gidanmu da take nakudar haihuwa domin mu taimaka mata sai kawai muka ga wuta kuma babu wani abu mai alamar wuta a dakina domin ko fitilar kwai ba ni da ita. Wannan wani al’amari ne daga Allah, suke nan guda hudu Allah Ya ba ni kuma Ya karbe abinSa ina fatan jama’a su taya ni da addu’a Allah Ya ba ni karfin halin jure rashin ’ya’yana Ya samin natsuwa.”