Malamin Islamiyya ya yi wa dalibansa 4 ’yan gida daya fyade a Gombe

Wasu mutum huku da suka yi wa yara ’yan gida daya fyade a Jihar Gombe, su ma sun shiga hannu

Malamin Islamiyya ya yi wa dalibansa 4 ’yan gida daya fyade a Gombe

Wani malamin makarantar Islamiyya ya shiga hannu kan zargin yi wa dalibansa mata hudu ’yan gida daya a fyade a Jihar Gombe.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce daliban Islamiyyar da malaminmu ya yi wa fyade sun hada da ’yar shekara takwas, ’yar shekara tara da mai shekara 12 da kuma mai shekara 14.

Kakakin rundunar, ASP Mahid Abubakar, ya ce an cafke malamin mai shekara 38 ne a ranar 7 ga watan Maris bayan mahaifin yaran ya kai karar fyaden da malamin yi wa ’ya’yansa a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

“Malamin, wanda mazaunin unguwar Malam-inna  da ke Gombe ya yi wa yaran fyade ne a makarantar Islamiyya da ke ungwuar.

”An kai yaran asibiti domin yi musu gwaji,” in ji sanarwar rundunar, wadda ta ce malamin Islamiyyar ya amsa laifin da ake zargin da ake tuhumarsa da aikatawa kuma nan gaba za a gurfanar da shi a kotu.

Abubakar  ya kara da cewa an kama wasu mutum uku da ake zargi da yin fyade ga wasu yara uku ’yan uwan juna masu shekara 12, 15 da kuma 17.

Ya ce mahaifain yaran ne ya kai karar mutanen masu shekara 50, 40 da kuma 30 kuma su ma sun amfa zargin da ake musu na yi wa yaran fyade.

Ya csu su ma zan gaba za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yanke musu hukunci.

A cewarsa, rundunar na aiki domin tabbatar da kariya ga kananan yara da matasa daga miyagu, inda ya yi kira ga jama’a da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanai.

“Rundunarmu na kira ga iyaye da su kasance masu kula da ’ya’yansu, musamman yara mata, a gida da makaranta ko idan an aike su ko a wurin wasa.”

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda