Malamin makaranta na so zama ba dan jarida ba – Lawal Yusufu Saulawa
Aminiya: Takaitaccen tarihinka? Lawal Saulawa: Assalamu alaikum, sunana Muhammadu Lawal Yusufu, amma da na fara aikin rediyo sai sunan Muhammadu ya bace, sai Saulawa ya shigo, wato sunana ya koma Lawal Yusufu Saulawa.Aminiya: Me ya jawo hakan?Lawal Saulawa: Abin da ya faru shi ne lokacin da na fara aikin rediyo akwai wani Injiniya shi ma […]
Aminiya: Takaitaccen tarihinka?
Lawal Saulawa: Assalamu alaikum, sunana Muhammadu Lawal Yusufu, amma da na fara aikin rediyo sai sunan Muhammadu ya bace, sai Saulawa ya shigo, wato sunana ya koma Lawal Yusufu Saulawa.
Aminiya: Me ya jawo hakan?
Lawal Saulawa: Abin da ya faru shi ne lokacin da na fara aikin rediyo akwai wani Injiniya shi ma sunansa Muhammadu Lawal Yusufu. Lokacin ana aikewa da wasiku ta gidan waya, kimanin shekara 50 da suka wuce, idan wasikunmu suka zo, shi yana injiniya a tashar FRCN da ke garin Jaji, ni kuma ina nan Kaduna. Sai wasikata ta tafi wurinsa, ko tashi ta zo wurina. To da ma mahaifina sunansa Yusufu Saulawa, ka ji dalilin da ya sa sunana ya sauya. An haife ni a watan Yunin 1945 a garin Saulawa da ke Jihar Katsina. Na yi makarantar firamaren Kayalwa, daga nan na wuce babbar firamare ta Funtuwa a 1960, muka kammala a1964 bayan mun rubuta jarrabawar WAEC. Na so na zama malamin makarantar kamar mahaifina, amma hakan bai tabbata ba saboda wasu matsaloli da suka bijiro min a lokacin.
Na fara aiki da wani kamfanin Inshora mallakin gwamnatin Jihar Arewa da wani kamfanin kasar Ingila . Batun sha’awata da aikin rediyo kuwa, ya samu tushe ne a wani lokacin ina aji biyu na makarantar sakandare, sai mahaifina ya tafi karatu kasar Ingila, inda daga can ya aiko min da karamin rediyo. Wannan ya sa nake sauraren gidajen rediyo daban-daban kamar su: Gidan Rediyo Tarayya da BBC da sauransu, daga nan sai sha’awar aikin rediyo ya shiga zuciyata matuka. Da farko na so na fara aikin rediyo ne, amma Ubangiji bai nufa ba. Sai na tafi wannan kamfanin inshora, na fara aiki da shi. Bayan na yi wata guda a Kaduna, sai aka tura ni hedkwatarsa da ke Legas. Ina can ne aka yi juyin mulkin farko a kasar nan wato juyin mulkin 1966. Wannan ya sa aka samu rikice-rikice nan da can. Kuma ya sanya su kansu kamfanin inshora suka fara nuna damuwarsa dangane da lafiyata. Saboda ni kadai ne dan Arewa da ke aiki da kamfanin a lokacin. Sauran abokan aikina daga Turawa sai mutanen Kudu. Daga nan sai suka yanke shawarar ba ni kudin mota na dawo Kaduna, amma ba da nufin na dawo na ci gaba da aiki ba. Saboda aikina irin na hedkwata ne ba na sauran ofishohinsu ba. Sai suka ce na yi tahowata za su ce saboda barazanar tsaro na gudu ka san Bature da wayo. Har ila yau, akwai wata rana na dawo hutu gida lokacin ina aiki da kamfanin sai wani jami’in gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna wato Alhaji Sani Katsina, ya gan ni a gaban mahaifina, ya bayyana masa cewa ina aiki ne a Legas. Ya ce duk da wannan tashin hankalin da ke faruwa, sai ni kuma na ce da ma ni wallahi a gidan rediyon na so na yi aiki, amma sai Allah bai ba ni ba. Sai ya ce kana so har yanzu, na ce eh. Sai ya ce to, rubutu, na rubuta, na ba shi.
Bayan na dawo daga Legas saboda tsoron barkewar rikici, sai aka kira ni a gidan rediyon FRCN, aka ce zan yi aikin daukar hoto ne a tashar talabijin. Da na je sai na ce musu ni magana nake so na yi a talabijin. A karshe sai na yi hakuri na karba haka na fara aikin mai daukar hoton bidiyo a ranar 15 ga watan Maris na 1967.
Shekara ta uku ina wannan aiki, akwai wani shiri na Adamu Salihu, mai suna Zakaranka Rakuminka, wanda yake magana kan aikin gona. Sai sukan ba ni matsayin Malamin Gona a shirin. Daga nan sai suka fahimci cewa na iya karatun Hausa sosai. Wannan ya sa Ladan Kwantagora shi kuma lokacin yana yin shirinsa na Maigida Barka da Rana, sai ya jawo ni na rika karanta masa wasiku, ka ga dai na fara magana. Shi kuma dan Iyan Zazzau Malam Yusufu Ladan, yana rubutu wasan Zaman Duniya Iyawa da Basabce, ana sanya ni irin wadannan shirye-shiryen. Ina cikin haka sai aka nemi ma’aikata a sashen rediyo wato masu gabatar da shirye-shirye, amma babu. Allah Ya jikan marigayi dahiru Modibo, sai ya yi magana da shugaban sashin talabijin. Ya ce “Yaron nan da ke aikin daukar hoto, domin Allah ba za ka ba ni shi ba.” Sai ya kira ni ya bayyana min abin da ke faruwa. Daga nan ne sai na dawo bangaren rediyo a 1970.
A lokacin da na dawo bangaren rediyon, sai aka ba ni ayyuka kamar na gabatar da shirye-shirye da shirya su da sauransu. Ina cikin haka sai na rubuta jarrabawar tafiya sashin Hausa na BBC. Kafin wannan sai Alhaji Tanko Yakasai lokacin yana Minista a gwamnatin Janar Yakubu Gowon, ana neman ma’aikata a gidan Rediyon China, ni ban san yadda aka yi ba sai ya ba da sunana domin ni dai ban san shi ba ma. Amma kawai sai na ga takarda cewa suna bukata ta. Har ila yau, a lokacin na rubuta jarrabawa da gidan rediyon Deutsche Welle, sai duka uku suka bukace ni. Amma na BBC sai suka ce min sun dauke ni aiki, amma ba zan fara ba, sai bayan shekara guda saboda a lokacin ne wa’adin aikin wanda zan maye gurbinsa zai kare. Sai mahaifina ya ba ni shawara da na yi hakuri na ta fi BBC, ya ce jiran shekara guda ba wani abu ba ne. A lokacin da na tafi na yi sa’a saboda wadanda suka tafi kafin ni, sai sun ajiye aikinsu. Amma daga kaina sai aka ce an ba da arona ne ga BBC na tsawon shekara uku. Na bar Najeriya zuwa Ingila ranar 13 ga watan Agustan 1973. Kuma ranar 12 ga watan Agustan 1976 na gama aiki da BBC. A wannan daren ban kwana a birnin Ladan ba, na dawo Najeriya.
Aminiya: Akwai wani shiri da za ka ce ka fi kauna cikin shirye-shiryen da ka gabatar?
Lawal Saulawa: Kafin na tafi BBC ni ne nake shirya shirin Barka da Yau, amma a lokacin shiri ne da ya yi kama da Jakar Magorin yanzu. Da na je BBC na ci gaba da karatu saboda suna taimaka wa ma’aikata. Kuma na yi karatun ne a bangaren Hulda da Jama’a. Ina aiki, ina karatu, amma lokacin da na fara aiki na gaji marigayi Fatahu Abdullahi ne wanda yake gabatar da shirin Labarin Wasanni. Wannan ya ba ni damar kewaye kusan duk wani filin wasa da ke birnin Landan ba wanda ban taba shiga ba. Daga nan sai na kirkiro wani shiri, mai suna dan Arewa a Landan. A wasan Sarkin Maska Mainasara Idris shi ne dan Arewan. A lokacin da shi da Alhaji Bashir Tofa (wanda ya taba tsayawa takarar Shugaban kasa) suna karatu a Birtaniya. Shi Bashir ya riga Sarkin Maska zuwa can. Ka san idan aka samu sabon zuwa wuri, dan gari shi ke sanya shi bisa hanya. Haka muka gabatar da wannan wasan kusan tsawon shekara biyu. Ba zan manta ba, lokacin da BBC ta cika shekara 50 da kafuwa a shekarar 2007, na ji sun sanya wannan wasan.
Bayan kammala aiki da BBC a 1976, sai dahiru Modibbo ya ce me sa ya ba za mu mayar da shirin Barka da Yau kamar shirin harshen Ingilishi, mai suna The World Today ba, musamman ma saboda yadda muke da wakilai ko’ina. Daga nan sai muka fara yin hakan ba tare da wani bata lokaci ba. Ni ne na fara shirin Barka da Yau wanda ake yi yanzu tare da labaru da rahotanni. A 1978, sai Gwamnatin Mulki Soji ta Murtala Muhammad ta yi alkawarin mika mulki ga farar hula. Aka ce an kwashe shekaru masu yawa ana mulki soja, jama’a sun fara mantawa da mulkin farar hula. Sai aka yanke shawarar kirkiro wani sabon shiri, mai suna Mece ce Siyasa. Alhaji Halilu Getso shi ne ya fara gabatar da shi. Sai aka ce wakilanmu duka suna Arewa ne, akwai bukatar a samu wakilai a yankin kudancin kasar nan. Daga nan sai aka tura ni garin Ibadan da ke Jihar Oyo, inda na yi kimanin shekara daya da rabi a can. Daga bisani aka kara yi mini sauyin aiki zuwa Jihar Legas, dadin zaman Legas shi ne ina tare da Shugaban kasa da kuma ’yan majalisu. Musamman ganin yadda ofis dinmu yana bakin zauren majalisa. Hakan ya sa ofis din ya zama kusan matattarar duka ’yan majalisunmu na yankin Arewa. Irin su Gwamnan Jigawa Sule Lamido suka zama kamar abokanmu a lokacin. Har ila yau, aikina a Legas ya ba ni damar kasancewa da Shugaba Shehu Shagari, saboda haka duk inda ya taka a fadin duniya tare muke tafiya. Hakan ya ba ni dama sosai wajen fahimtar bangarorin duniya daban-daban, kasan masu iya magana na cewa tafiya mabudin ilimi.
Aminiya: Wadanne kalubale ne ba za ka manta da su ba a aikin jarida?
Lawal Saulawa: Wato gwargwadon iko na yi aiki da mutane natsattsu saboda haka kusan duk abin da muka yi mun yi shi ne gwargwadon iko. Kuma shugabanninmu sun sanya mu a kan hanya sosai. Ba zan iya cewa ga wani abu wanda ya zamo mini kalubale ba. Sa’ar da na yi ita ce Allah Ya ba ni iko, kuma shugabannina sun ba ni dama ta yin abubuwa daban-daban cikin aikin rediyo. Kusan gaba daya aikin bangaren injiniya ne kawai ban yi ba. Kuma shi ma lokacin da na zama manaja na yi.
Aminiya: Wadanne manyan mukamai ka taba rikewa?
Lawal Saulawa: A lokacin gwamnatin Gwamna dangiwa Umar ya nada ni Kwamishinan Yada Labaru a tsohuwar Jihar Kaduna. Daga nan aka mayar da ni Kwamishina a Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu. Kazalika, lokacin da aka bai wa Katsina jiha, Kanar Sarki Mukhtar ya zama gwamnanmu na farko, ya nada ni Kwamishina a Ma’aikatun Kasuwanci da Masana’antu da kuma ta Yada Labarai. Ni ne na fara yin Manajan Darakta na gidan Rediyo da Talabijin din Jihar Katsina. Sai Shugaban Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, inda daga nan na yi ritaya. Kuma cikin ikon Ubangiji wurin da na fara aiki a karamin ma’aikaci a nan na kammala a matsayin babban ma’aikaci. Har ila yau a yanzu haka ni ne Shugaban gidan Rediyon Nagarta da kuma Rediyo Gotel da ke Jihar Adamawa.
Aminiya: Akwai wani abu da ba za ka manta da shi ba a aikin jarida?
Lawal Saulawa: Suna da dama, amma kadan daga ciki su ne: Damar da na samu ta aiki da gwamnatin Shehu Shagari da kuma yadda na san aikin kamar tafin hannuna.
Aminiya: Ko kana da magaji a aikin jarida?
Lawal Saulawa: Ah, yanzu haka dana Usman yana shekarar karshe a karatun aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano. Kazalika akwai wata ’yata Nafisa da ita ma take karatun aikin jarida a Jami’ar Abuja. Har ila yau, babban dana Abdullahi tun lokacin da nake aiki a Legas yake aiki da gidan rediyon Deutsche Welle. Ka ga alhamdulillahi akwai alamun samun magaji.
Aminiya: Wace shawara kake da ita ga matasa ’yan jarida?
Lawal Saulawa: Tabbas ba a rasa shawarwari ga matasa ’yan jarida, mukan dauko ta tun daga mai sha’awar aiki kan abubuwa uku. Na farko ka zama mai sha’awar aikin. Abu na biyu, Allah Ya ba ka dama, san nan idan ka shigo ka mayar da hankali, ka sadaukar da kai ka kuma jajirce. To shi ne za ka ga, ka ci nasara.
Aminiya: Batun iyali fa?
Lawal Saulawa: Ina da mata hudu (akwai guda daga cikinsu Bayarbiya, wacce na auro daga garin Ibadan) baki daya kuma ina da ’ya’ya 13.