Malamin Makaranta ya kashe dansa a Jigawa
Wani malamin makaranta mai shekara 55 da haihuwa da ke koyarwa a makarantar ’yan mata ta Malam Madori ya yi wa dansa dukan kawo wuka har ta kai ya yi sanadin mutuwarsa.Malamin mai suna Muhammed Bello mazaunin gidajan Siriya ne da ke cikin gidajan gwamnati na karamar Hukumar Malam Madori, tuni ya shiga hannun ’yan […]
Wani malamin makaranta mai shekara 55 da haihuwa da ke koyarwa a makarantar ’yan mata ta Malam Madori ya yi wa dansa dukan kawo wuka har ta kai ya yi sanadin mutuwarsa.
Malamin mai suna Muhammed Bello mazaunin gidajan Siriya ne da ke cikin gidajan gwamnati na karamar Hukumar Malam Madori, tuni ya shiga hannun ’yan sanda.
Shugaban Hukumar tsaro ta Cibil Defence Alhaji Muhammed Gidado wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce malamin ya yi amfani da itace ne ya yi wa dan munanan raunuka ya karya shi a hannu ya kuma fasa masa kai.
dan mai shekara 18 mai suna Dauda Muhammed yana karatu ne a sakandaren Malam Madori kuma lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da matar mahaifinsa mai suna Jummai Mohammed ta fada wa mijinta cewa Dauda ya ki debo ruwan da zai isa girki a gidan, shi kuma sai ya harzuka ya dauki ita ce ya rika dukan dan nasa har wanda ya fadi a kofar gidansu ya suma.
Jami’an Cibil Defence ne suka dauki matashin zuwa asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Shugaban Hukuma Cibil Defence din ya kara da cewa jami’ansa sun mika mahaifin yaron ga ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
A karamar Hukumar Kazaure kuwa jami’an na Cibil Defence sun tsinci gawar wani yaro mai kimanin shekara 12 mai suna Nura Abdullahi ne da ke ajin karshe a Makarantar Firamare ta Arewa a Kanti Kazaure a cikin wani tafki.
Wata majiya ta ce Nura ya fada a tafkin ne yana wasan linkaya shi da abokansa sai ya fada wuri mai zurfi ya kasa fitowa daga baya aka tsinci gawarsa.