Malamin sakandare ya yi wa surukinsa dukan kawo wuka

Wani malamin makarantar sakandare mai suna Muhammadu wanda aka fi sani da Na-ala-ala ya lakada wa surukinsa wato mahaifin matarsa mai suna Umaru Garba mai kimanin shekara 65 dukan kawo wuka.Surukan suna zaune ne a Unguwar Hanwa da ke karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya Jihar Kaduna.Aminiya ta iske dattijo Umaru Garba wanda ya sha […]

Malamin sakandare ya yi wa surukinsa dukan kawo wuka

Wani malamin makarantar sakandare mai suna Muhammadu wanda aka fi sani da Na-ala-ala ya lakada wa surukinsa wato mahaifin matarsa mai suna Umaru Garba mai kimanin shekara 65 dukan kawo wuka.
Surukan suna zaune ne a Unguwar Hanwa da ke karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya Jihar Kaduna.
Aminiya ta iske dattijo Umaru Garba wanda ya sha duka a hannun surukinsa ya kai kara Babban Ofishin ’Yan sanda da ke Shiyya ta daya a Zariya domin a shiga tsakaninsu da mijin ’yarsa.
Malam Umaru Garba ya yi wa Aminiya bayanin sanadiyyar dukansa da mijin ’yarsa ya yi, inda ya ce ni asalina mutumin Zamfara ne, shekara 45 da suka wuce na zo ci-rani garin nan kuma Allah Ya yi min zama a wannan unguwa ta Hanwa, Allah Ya yi min arziki na fara tireda.”
Ya ce surukin nasa shi shi ne yaronsa na farko da suka fara wannan kasuwanci da shi lokacin yana karatu, “Kusan ni nake biya masa kudin makarantarsa kuma bayan shekarun da muka yi tare muna zaman lafiya ne na dauki babban ’yata na ba shi aurenta kuma yanzu haka ’ya’yansu 10, kuma duk suna raye hasali ma aikin da yake yi yanzu a Zamfara ’yan uwana suka nema masa, ni kuwa yanzu ba na komai sai aikin gadi, saboda ya nemi wata biyan bukata kuma na ga abin bai yiwuwa daga nan fa sai gaba ta kullu tsakaninmu.”
Ya ce bukatar ita ce “Wata rana yana zaune a daki sai ya same shi ya ce wai yana bukatar zai wanke al’aurana ya tari ruwan wai zai hada min wani asiri da shi, ni kuma a sanina shi ba malami ba kuma ba boka ba, cikin mamaki na ce masa ka taba ganin inda aka yi haka, ka tuna fa ni surukinka ne ’yata kake aure sannan ka ce in bude maka gabana ka wanke, to, Allah Ya kyauta ba zai taba yiwuwa ba. To tun daga nan ya kullaci gaba da ni da iyalina, a daren Talatar nan ya same ni har cikin daki ya ce in saki matata uwargidan. A kan na ki ne ya hauni da duka kamar zai kashe ni har sai da makwabta suka kwace ni, kuma ya ce sai ya ga bayana ni da iyalina don haka na kawo kararsa nan domin a shiga tsakaninmu da shi,” inji shi.
Da Aminiya ta nemi jin ta bakin wanda ake zargi da dukan surukinsa, Muhammadu Na’ala-ala ya musanta wannan zargi a inda yace yana yi wa surukinsa dukkan biyayyar da ta dace kuma matarsa ta san duk irin kokarin da yake yi wa mahaifinta.
Ita kuwa matar Muhammadu mai suna Hauwa wanda akab fi sani da ’Yar Bello ta ce ita a saninta mijinta ba zai taba aikata abin da aka ce ya yi ba, hasali ma ma kwanan nan ya aurar da kannenta mata biyu. Ta ce sun haifi ’ya ‘ya goma tare da shi, illa Shaidan ne kawai ke neman ya mutsa zumuntar da ke tsakaninsu.
Hukumar ’yan sanda ta sasanta tsakaninsu tare da jan kunnensu cewa su zauna lafiya su daina neman tona wa kansu asiri.