Malan Muhammad Buhari kusugu Daura

Sanarwar da sabon Shugaban kasa mai jiran gado ya bayar ta kankare lakabin ‘Janar’ daga sunansa da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga wanan wata, abu ne da ya dace da sabon matsayinsa. Ya bukaci a rika kiransa Muhammadu Buhari, Shugaban Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, ba dadi, ba kuma ragi. Haka nan kuma […]

Malan Muhammad Buhari kusugu Daura
Malan Muhammad Buhari kusugu Daura

Sanarwar da sabon Shugaban kasa mai jiran gado ya bayar ta kankare lakabin ‘Janar’ daga sunansa da zarar an rantsar da shi a ranar 29 ga wanan wata, abu ne da ya dace da sabon matsayinsa. Ya bukaci a rika kiransa Muhammadu Buhari, Shugaban Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, ba dadi, ba kuma ragi. Haka nan kuma sanarwar da aka bayar dangane da haka ta nuna cewa shi ma mataimakin Shugaban kasa za a rika kiransa Farfesa Yemi Osinbanjo SAN. Haka nan kuma an fitar da sabon hoton Muhammadu Buhari a matsayin wanda za a yi amfani da shi a hukumance, wanda kuma za a sarkafe a dukkan ofisoshin gwamnati da sauran wuraren da ya kamata. Wannan hoto ya nuna Muhammadu Buhari cikin rigar agbada, ko kuma a ce shakwara da wata tagiyar Zanna Bukar mai launoni iri iri, da gilashin idanu.

Wannan dai ba sabon abu ba ne ga jama’ar Najeriya domin an ga haka a zamanin da Olesegun Obasanjo wanda ya komo kan karagar mulki a matsayinsa na farar hula a 1999. Shi ma ya bukaci a cire masa lakabin Janar daga sunansa a lokacin, a maye hakan da lakabin Cif, abin da ake kiran duk wani mutumin Kudancin kasar nan da ya kasaita. Haka nan kuma an samar da hoton Cif Olusegun Obasanjo sanye da sutura irin ta ‘yan kabilarsa, Yarbawa da wata hula mai kama da guntun sanho da ake lankwashe ta a gefen hagu. Kuma tun daga wancan lokacin an daina kiran Cif Olusegun Obasanjo da lakabin Janar, duk kuwa da cewa wani lokaci yakan gwada halaye da babi’u irin na Janar idan tsohuwar allurarsa ta soja ta motsa.
Har yanzu dai ‘yan Najeriya ba su fahimci hikimar kawar da lakabin Janar ba daga sunayen tsoffin sojojin da suka taba jagorantar gwamnatin mulkin soja. Amma sai dai wasu suna cewa hakan bai rasa nasaba da yadda jama’a suke kyamatar gwamnatin mulkin soja don haramcinta da kuma yadda ba a kaunar Shugabanninta saboda rashin tuntubar jama’a wajen gudanar da harkokinsu. To amma hakan bai hana tsofaffin sojojin tsunduma cikin harkokin siyasa ko tsoma bakunansu cikin al’amuran da suka shafi jama’arsu da kuma dagewa lallai sai an bi son zukatansu ba. A nan Najeriya ne ake haka kawai, a sauran kasashen duniya tsofaffin sojojin da suke mulkin kasashensu ana kiransu da lakabinsu, suna kuma alfahari da haka.
To, mun ji wannan! Bari kuma mu waiwayi yadda bayan Olusegun Obasanjo ya yi watsi da lakabin Janar bayan darewarsa mulki ya rarumo lakabin Cif, aka yi ta kiransa da shi. Haka nan kuma sanarwar da aka bayar don cire lakabin Janar daga sunan Shugaba Muhammadu Buhari ta nuna cewa ana iya kiran mataimakinsa da lakabin Farfesa. To shi Muhammadu Buhari da wane lakabi ke nan za a ci gaba da kiransa, ko kuwa babu ne? Haka nan za a dinga kiransa sunansa gatsau, tsirara, ba a sakayawa? Idan har za a kira Olusegun da lakabin Cif, dai-dai da al’adar jama’arsa, ai mu ma a nan muna da lakabi masu armashi wadanda za su dace da sabon matsayin Muhammadu Buhari. Akwai mu da lakabin Malam, sa’annan kuma akwai lakabin Alhaji, wanda kuma duk aka kira shi da shi ya dace matuka. Amma na tabbata jama’a zai fi son kiransa da lakabin Malam, domin kuwa wannan kalma ce ta girmama mutum, kuma wanda duk ya daukaka, ana kiransa haka. Misali shi ne Malam Abubakar Gumi, da Malam dahiru Bauchi da Malam Aminu Kano da Malam Abubakar Imam da Malam Umaru ‘Yar’adua da Malam Nasiru el-Rufa’i da Malam Ahmadu Ribadu da Malam Abubakar danmusa, dukkansu ana kiran kowannensu Malam domin ya cancanci haka. Saboda haka nan zai fi kyau idan an kara wa Muhammadu Buhari da lakabin Malam a rika kiransa da haka, don wannan ne ya fi cancanta.
Bayan haka nan kuma duk wani Shugaban Najeriya, walau na soja ne ko na farar hula yana da sarautar gargajiya, wacce Sarkin garinsu ya nada masa ita, amma ban da Malam Muhammadu Buhari. Shi har yanzu kansa tsirara yake, ba rawanin wani sarki da ke sakaya shi. Shi ya sa wannan fili na Matashiya yake ganin zai dace matuka idan Malam Muhammadu Buhari zai daure, ya dage, ya ciccije, ya mance da abubuwan da suka hana shi mika wa wani Sarki kansa don a nada masa rawani; ya amince da sarautar da talakawa za su bukaci Sarkin Daura ya nada masa, watau ta Kusugun Daura.
Dalilin haka kuwa shi ne Daura ce tushen Hausa, kuma a nan ne aka samu rijiyar Kusugu mai cikakken tarihi, wacce jama’a ke amfana da albarkatunta, amma akwai wani maciji da ke hanawa, sai rana-rana ake diban ruwanta. Daga bisani an samu wani jarumi, mai suna Bayajida wanda ya kashe macijin, ya tserar da jama’a daga wahalhalun da ke janyo masu kuncin rayuwa. To wannan rijiyar ita ce Najeriya, macijin kuma jam’iyyar PDP da Shugabanninta. Malam Muhammadu Buhari ne kuma ya kwatanta abin da Bayajida ya yi na kashe wannan maciji da ake kira ‘Sarki’ , wanda ya addabi jama’a, domin shi ne ya kawar da Maimalfa daga bisa tasa sarautar da ya yi amfani da ita don gallazwa jama’a.
Ashe ke nan rijiyar Kusugu ita ce ta yi sanadiyyar habakar tarihin kasar Hausa kafatan, wacce a ciki aka kashe ‘Sarkin” da ya hana jama’ar Daura sakat, hakan kuma ya yi dai-dai da bayyanar Malam Muhammadu Buhari a Najeriya. To tun da shi dan Daura ne, me zai hana ba za a ba shi sarautar Kusugun Daura ba, a matsayin tukwuicin abin alherin da ya janyo wa Najeriya? To bayan mun kammala tsalle da murnar rantsuwa a Abuja, muna kuma jiran halartar bikin nadin Kusugu a fadar Mai martaba Sarkin Daura. Tun yanzu jama’a ma sun fara sauya lakabin GMB da MMB , suna kuma gaisuwa, suna cewa: “A gaishe ka Malam Muhammadu Buhari, Kusugun Daura.”