Maleriya: Mutum milyan 2.8 Suka je asibiti a Kano a 2021

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutum milyan 2.8 da suka je asibiti saboda zazzabin cizon saura a jihar 2021. Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Tsanyawa, ne ya bayyana hakan inda ya ce kashi 60 a cikin 100 na masu zuwa asibiti suna zuwa ne saboda cutar zazzabin cizon sauro da suka yi […]

Maleriya: Mutum milyan 2.8 Suka je asibiti a Kano a 2021

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa akalla mutum milyan 2.8 da suka je asibiti saboda zazzabin cizon saura a jihar 2021.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Aminu Tsanyawa, ne ya bayyana hakan inda ya ce kashi 60 a cikin 100 na masu zuwa asibiti suna zuwa ne saboda cutar zazzabin cizon sauro da suka yi fama da ita.

Kwamishinan Lafiyan ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai ranar Litinin, wadda ta kasance Ranar Zazzabin Zizon Sauro ta Duniya ta 2022.

Ya bayyana cewa daga watan Yuli zuwa Oktoba a 2021, gwamnatin jihar tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki, sun raba magunguna riga-kafin cutar akalla 13,110,365 a wani yunkuri na yakar ta, musmman ga kananan yara ’yan kasa da shekaru biyar.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su tabbata sun kai ’ya’yansu ’yan wata 3 zuwa 59 da haihuwa a wani shirin rarraba magungunan riga-kafin cutar da za a yi na tsawon kwana hudu.

Ya kara da cewa akalla yara milyan 3,193,002 ake sa ran za su amfana da wannan riga-kafin wanda ake tunanin zai magance matsalar cutar da kaso 75 a cikin 100.