Maleriya ta halaka yarinya a hanyar zuwa asibiti

Wata yarinya mai shekara daya da wata bakwai mai suna balentina Godwin ta gamu da ajalinta, a daidai lokacin da ake hanyar kai ta asibiti, bayan da ta harbu da cutar zazzabin cizon sauro. Lamarin wanda ya faru a garin Kubwa a makon jiya, ya jawo alhini a bangaren yara na babban asibitin Kubwa, inda […]

Maleriya ta halaka yarinya a hanyar zuwa asibiti
Maleriya ta halaka yarinya a hanyar zuwa asibiti

Wata yarinya mai shekara daya da wata bakwai mai suna balentina Godwin ta gamu da ajalinta, a daidai lokacin da ake hanyar kai ta asibiti, bayan da ta harbu da cutar zazzabin cizon sauro.

Lamarin wanda ya faru a garin Kubwa a makon jiya, ya jawo alhini a bangaren yara na babban asibitin Kubwa, inda aka garzaya da yarinyar, a sakamakon kukan da mahaifiyarta ta rika yi a yayin da kanwar uwar kuma ta rika yin addu’o’i da karfi a kan gawarta, tare da begen ganin yarinyar ta motsa.

Mahaifin yarinyar mai suna Mista Ekunwi Godwin ya ce sun kula da rashin lafiyar yarinyar ne a ranar Laraba, bayan jikinta ya yi dumi sannan ya kara muni bayan dan lokaci inda ta rika yin masassara. A cewar mahaifin, “nan take na garzaya da ita karamin asibitin garin Dutsen-Alhaji inda muke da zama, sannan likita ya duba ta tare da ba ta magunguna.

“Sai dai lamarin ya sake tashi a yau Alhamis kuma bayan mun koma asibitin ne sai aka turo mu nan, sai dai kafin mu karaso sai muka kula da ’yar tamu ta daina yin motsi,” inji mahaifin.

Likitan da ya tabbatar da mutuwar yarinyar bayan tantance ta, ya shawarci iyaye da su rika kai ’ya’yansu manyan asibitoci a maimakon kanana, idan zazzabinsu ya kai matakin masassara, wadda ya ce ke faruwa ga kananan yara a lokacin da zafin jikinsu ya kai matakin digiri 38. Ya kuma bayyana mamakinsa a kan rashin ayyana dokar ta baci a kan cutar daga bangaren Gwamnatin Tarayya; ta hanyar gudanar da bincike na musamman tare da samar da magunguna masu aiki don magance cutar, wadda ya bayyana a matsayin annoba a halin yanzu.