Malesiyawa 12 sun keta kasashe 12 daga kasarsu zuwa Saudiyyya a kan babur

Mutum 12 ’yan kasar Malesiya, sun tashi daga baban birnin kasarsu, Kuala Lumpur, a kan babura takwas, suka yi ta tafiya har suka keta kasashen duniya 12, sun kuma shiga birane 53, sannan suka sauka a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.Wannan tafiya a kan babur, mutanen Malesiya sun yi ta ne cikin kwana 60.Taron […]

Malesiyawa 12 sun keta kasashe 12 daga kasarsu zuwa Saudiyyya a kan babur
Malesiyawa 12 sun keta kasashe 12 daga kasarsu zuwa Saudiyyya a kan babur

Malesiyawa a MadinaMutum 12 ’yan kasar Malesiya, sun tashi daga baban birnin kasarsu, Kuala Lumpur, a kan babura takwas, suka yi ta tafiya har suka keta kasashen duniya 12, sun kuma shiga birane 53, sannan suka sauka a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
Wannan tafiya a kan babur, mutanen Malesiya sun yi ta ne cikin kwana 60.
Taron Malesiyawan da ke zaune a kasar Saudiyya suka taru a wani otal don tarbar wadannan matafiya. Shugaban matafiyan ya bayyana wa shafin sadarwa na Sabak cewa wannan shi ne karo na uku da ya yi irin wannan tafiyar.
Matafiyan dai sun ce babu wata wahala ko matsala da suka fuskanta a wannan tafiya, sai dai wajen tsallaka kan iyakar kasashen da suka biyo ta ciki. Kuma  duk lokacin da suka shiga wata kasa, sai ofishin jakadancinsu ya yi kokarin gyara musu hanyar shiga kasar. “Jami’an tsaron kan iyaka ne kawai suka dan bincike mu,” a cewarsu. Wadannan matafiya sun yi wannan tafiyar ne don aikin umra.