Mali ta bai wa jakadiyar Sweden wa’adin ficewa daga ƙasar
Sweden ta ce ta daina bai wa Mali tallafi alhali tana goyon bayan Rasha.
Gwamnatin mulki soji a Mali ta bai wa jakadiyar ƙasar Sweden Kristina Kuhnel umarnin ficewa daga ƙasarta cikin awa 72.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ce ta sanar da hakan a ranar Juma’a, kan abin da ta kira “wasu kalamai marasa daɗi” da wani Ministan Sweden ya yi.
- Jawabin Tinubu: Babu wani kuɗin tallafi da aka raba wa jihohi — Gwamnan Oyo
- Za mu biya Julius Berger N280bn don kammalan titin Abuja zuwa Kano —Minsita
A ranar Laraba ce da Ministan Sweden na Ci Gaban Hadin Kan Kasa da Kasa da Kasuwanci, Johan Forssell, ya ce gwamnatin ƙasarsa ta yanke shawarar daina bai wa Mali tallafi.
Forssell ya faɗa a ranar Laraba cewa, “Ba za ku goyi bayan yakin zaluncin da Rasha ke yi ba bisa ka’ida ba a kan Ukraine, kuma a lokaci guda ku ci gaba da karbar miliyoyin kudi duk shekara don taimakon raya kasa ba.”
Forssell ya faɗi hakan ne a matsayin martani ga wani sako da aka wallafa a shafin X wanda ya ce Mali ta yanke hulda da Ukraine.
Kawo yanzu dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Sweden ba ta ce komai ba tukunna a kan batun.
A wannan mako ne Mali ta sanar da yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine bayan ta zargi mahukunta a birnin Kiev da goyon bayan ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ke da hannu a mummunan harin da aka kai wa sojojin ƙasar.
Ukraine ta ce ba ta ji dadin yanke alakar diflomasiyya da Nijar ta yi da ita ba, ’yan kwanaki bayan da makwabciyar Nijar, Mali ta dauki irin wannan mataki bisa zargin sojojin Ukraine da tallafa wa ’yan ta’adda.
Ukraine ɗin ta ce ta yi takaicin yadda mahukuntan Nijar suka yanke shawarar dagula alakar diflomasiyyar da ke tsakaninsu ba tare da sun gudanar da wani bincike kan gaskiyar abin da ya faru da jami’ansu da hukumomin Mali ba.
Tuni dai Mali da maƙwabtanta Nijar da Burkina Faso suka ƙulla alaƙa ta ƙut-da-ƙut da Rasha don tura haushi ga ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka Faransa, da Nijeriya da kuma Amurka.