Mallakar dukiya: Yau za a fara shari’ar Sanata Saraki

Yau za fara shari’ar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki bayan da Hukumar da’ar Ma’aikta  ta gurfanar da shi gaban kotu bisa zarginsa da aikata laifufuka 13 da suka hada da almundahana.karar mai lamba ABT/01/15, da kwanan wata 11 ga Satumba, an gabatar da ita ce a gaban Kotun da’ar Ma’aikata, inda ake zargin […]

Mallakar dukiya: Yau za a fara shari’ar Sanata Saraki
Mallakar dukiya: Yau za a fara shari’ar Sanata Saraki

Yau za fara shari’ar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki bayan da Hukumar da’ar Ma’aikta  ta gurfanar da shi gaban kotu bisa zarginsa da aikata laifufuka 13 da suka hada da almundahana.
karar mai lamba ABT/01/15, da kwanan wata 11 ga Satumba, an gabatar da ita ce a gaban Kotun da’ar Ma’aikata, inda ake zargin Sanata Saraki da yin karya wajen bayyana kadarorinsa a fom din Hukumar Kula da da’ar Ma’aikata da ya cike a lokacin da yake Gwamnan Jihar Kwara.
Tuhume-tuhumen da jaridar Premium Times ta fara fallasawa a shekaranjiya Laraba da safe, sun hada da zargin Sanata Saraki da kin bayyana dukiyar da ya samu ko ya saya a lokacin da yake Gwamna.  
Daga cikin laifuffukan da ake zargin Sanata Bukola Saraki akwai mallakar dukiyar da ta fi karfin samunsa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati – wato Gwamna da Sanata.
Laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa kamar sun saba wa Rataye na Biyar na Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kamar yadda aka gyara shi.
Kuma an zargi Sanata Saraki da saba wa sashi na 2 na dokar Hukumar da’ar Ma’aikata da Kotun da’ar Ma’aikata da za a iya hukunta shi a karkashin sakin layi na 9 na Rataye na Biyar na tsarin mulkin.
Mataimakin Darakta a ofishin Babban Lauyan Tarayya M.S. Hassan ne ya shirya tuhume-tuhumen. Kuma wani babban lauya da ya nemi a sakaye sunansa ya ce idan aka samu Saraki da laifi za a kwace kadarorin kuma ya bar majalisa tare da hana shi rike kowane mukami sai bayan shekara 10.
 Sai dai a martanin da ofishin Sanata Saraki ya mayar kan karar ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana su da karya kuma shirye sannan an sanya siyasa a ciki.
Sanata Saraki ya nuna mamaki kan yadda Hukumar da’ar Ma’aikatan ba ta  tado da wadannan zarge-zarge ba sai bayan shekara 12 sannan ya yi zargin akwai tufka da warwara a tuhume-tuhumen da ake yi masa.