Malun-malun

‘Malun-malun fankaceciyar taguwa,’ a cewar Malam mai yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba. Kuma duk wanda aka gani da sanye da malun-malun za a iya hanzarin cerwa yana cikin jerin masu koyar da watsatttsake da buda wagagen littattafai, uwa-uba sukan himmatu ka’in da na’in wajen kawar da juhala don tabbatar da adala. […]

Malun-malun
Malun-malun

‘Malun-malun fankaceciyar taguwa,’ a cewar Malam mai yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba. Kuma duk wanda aka gani da sanye da malun-malun za a iya hanzarin cerwa yana cikin jerin masu koyar da watsatttsake da buda wagagen littattafai, uwa-uba sukan himmatu ka’in da na’in wajen kawar da juhala don tabbatar da adala. A wannan karon ana ta hayagaga da masu malun-malun da suka karbi na-goro a hannun Malam Namando da kuma wani ba’ari da aka ce, an jinka musu Hauro malala gashin tunkiya, don su goyi bayan gudun loko da jona-tantin mulkin mulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge.

Batu na ingarman karafa, ya kamata mu fasko cewa, ulama’u, wato masana a cikin addinin kadaita Mahalicci da ibada su za su nusar da mu yadda ake kauce wa kwalama da kwaraka a wajen attajirai da masu mulki. Kodayake masana na sane da cewa, akwai tanadi na zakka da sadaka da hadiyya wadanda suka halatta a dokokin Mahalicci, amma a jinka wa mutum wani dan abin da bai taka-kara ya balla ba, zai iya zama haramun, musamman idan har abin da aka jinka wa mutum ba shi da muhalli a tanade-tanaden dokokin addini.
Ganin irin hantsal-batsala din da masu malun-malun ke yi a Arewacin Haurobiya. Ta sanya ya zama wajibi in nusar da masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya cewa, darasin wannan mako ba namu ba ne. Tun kafin a bijiro mini da tambaya kan matsayin darasin, bari in yi kandagarki da fadar Malam mai malun-malun, wato inda ya biya mana a cikin karatun azure, cewa: Koyon watsatttsake da buda wagagen littattafai ya zo gabanin fada da aiki.” Sannan a cikin wagagen littafin Malam Garzali, mai lakabin ‘Ya kai man kaza,” an Ambato cewa: “duk fannin ilimi da bai zamto na aiki a aikace ba, to ya zama hauka, shi kuwa aikin da babu sani a cikinsa, to ba zai taba kasancewa ba.”
Wani mashahurin masani da aka saba baje wagagen littattafai a gabansa, ya taba karonto mana kalaman fiyayyen halitta, Mai tsira da aminci, cewa: Fushin mahalicci yana tabbata a kan bawa, wanda suturarsa ta fi aikinsa kyau. Domin tufafinsa (malun-malun dinsa) kamar ta Mazannin Mahalicci, amma ayyukan da yake tsuwurwurtawa irin na kangararru ne a cikin al’umma.”
Hakika idan ahr za a yi batun da babu waskiya a cikinsa, kowa zai fahimci cewa, hayagagar karbar nagoro da ake yi manyan masanan Addinin Kadaita Mahalicci da ibada, za a iya dorata bisa ma’auni, kuma a yanke hukuncin cewa, wanda ya karbi awalaja, don ya taimaka wajen wujijjiga rayuwar Haurobiyawa, ya aikata ta’asa a kwanon tasa, don haka kangararre ne, wanda malun-malun dinsa ta fi ayyukan da yake tsuwurwurtawa kyawun gani. Mai irin wannan ta’asa ya kamata ya yanke wa kansa hukunci, inda zai iya bijiro da tambayar bin bahasin ko ya hadu da fushin Mahalicci?
Kuma wanda duk ya wancakalar da saninsa, ya mayar da hankalinsa a hannun malun-malun, saboda kwalama da kwarakar abin duniya ko soyewar zukata, shi ma ya kamata ya fasko matsayinsa?
Watakila wani daga cikin manyan malumma masu malun-malun da aka jinka musu ’yan matsabbai don su kafa ruhin dama-dama-da-kurda-kurdar was an Samson-siya-siya a zukatan masu ibada, wani zai ce ai akwai takwarorinmu da ke jagorantar wani ba’ari na mutane a majami’u da aka ce an jinka musu Hauro gashin balama kwanciyar magirbi, ka ga ke nan, mu ma kada mu bar bati. Masu irin wannan tsari na karatun waskikar jakin-dawa da na gida, akwai bukatar su fasko cewa, sakaci da sakarcinsu wajen nusar da masu mulki dabarun kawar da juhala da tabbatar da adala ya jefa Haurobiyawa cikin rudani.
Yau an wayi gari ’yan adawa sun daina shiga dawa, amma ga masana da ake kyautata wa zaton suna da kusanci da Mahaliccinsu sun fantsama cikin kungurmin daji, inda suke agaza wa wadanda suka jefa al’umma cikin duhun-dundum-durun-dum, har kasa ta zama jamhuriyyar ja-ni-in-reto, tamkar dai yadda muka sha bijiro muku a daukacin darusssanmu. Sun zuba wa samarin kusu da ’yan matan jaba na-mujiya. Kai kowa ya san Namando ba masanin addini ba ne, domin ni har yanke cewa, ‘bai san bihim ba,’ amma yau sai ga manyan masu malun-malun da suka nannagi darussan karatu a wagagen littattafai suna mai kanannen gannai, har sai ya afka su cikin rami. Ni dai ban yi mamaki ba, domin na sha jin masana da ke tsoron Mai-duka sun karaton daga babban littafi cewa, irin wannan rukuni da suka yi watsi da saninsu, “tamkar aura ne dauke da mangala littattafai.’
Ta yi wu saboda ni direban alli a farfajiyar Dodorido shi ya sa nike ganin wallen masu jinka wa masanan addini awalaja don su cefanar da mabiyansu. Wanda duk yake ganin makarantarmu na goyon bayan jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu, shi yasa muke adawa da awalajar da aka jinka musu, to kamarta ya yi ya jagoranci sauran masu malun-malun, don su ma a cika musu damin Hauron su har su tsakuri Hauro gashin balama kwanciyar magirbi, kamar yadda aka bai wa takwarorinsu a kungiyar masu ibada a majami’u.
Haurobiyawa kowa ya shiga taitayinsa, domin an batar da gungun masana, har hankalinsu ya tare a hannun malun-malun. Idan kuwa muka ci gaba da bin su a makance, to za su kai mu su baro. Tuni dai muka samu labarin cewa, wasu da suka samu camamarsu har sun fara yi wa jam’iyya mai dan boto da sanda jirge yakin neman zabi-sonka. Ni ina ganin da ba masu hankali a hannun malun-malun bane, sai su dauki fatawar marigayi Aminin siyasar mutanen birnin Dabo, wanda ya taba bayyana wa magoya bayansa a jam’iyyar dan mabudi cewa, ‘idan masu mulki suka jinga musu ’yan matsabbai ko wasu kyaututtuka dab a su saba yi muku ba, sai don jan ra’ayinku a lokacin da zabi-sonka ke karatowa, to ku karba, amma kada ku kuskura ku kada musu kuri’unku.
Mafita dai mu goyi bayan abin da yake daidai, mu kuma yi nesa da batan-baka-tantan!