Mamallakin Manchester City ya zama Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa

Kafin nadin nasa dai, attajirin shi ne Mataimakin Fira Ministan kasar

Mamallakin Manchester City ya zama Mataimakin Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa

Sheikh Mansour Bin Zayed

Hadaddiyar Daular Larabawa ta nada mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City da ke Ingila, Sheikh Mansour bin Zayed a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Kasar.

A cikin wata sanarwa da kamfanbin dillancin labaran kasar na Wam ya wallafa, kasar ta ce attajirin ya dare kujerar ce a matsainsa na shugaban gwamnati.

Shugaban Kasar ne dai ya sanar da amicewar nadin, inda ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Kolin Kasar na nada Sheikh Mansour a matsayin.

Kafin nadin nasa dai, attajirin shi ne Mataimakin Fira Ministan kasar.

Bugu da kari, Shugaban Kasar ya ayyana sunan dansa, Sheikh Khaled bin Mohamed bin Zayed, a matsayin Yarima mai jiran gadon Abu Dhabi, wacce ita ce masarauta mafi arziki a jerin masarautun kasar bakwai.

Hakan dai na nufin dan nasa shi ne zai kasance mai jiran gadon sarautar kasar bayan mahaifinsa.

Shiekh Mansuor dai ya taba zama Mataimakin Fira Minista kuma Shugaban kotun kasar, tare da rike wasu gwababan mukamai musamman a bangaren kasuwanci.

A watan Mayun bara ne dai aka ayyana Sheikh Mohamed bin Zayed a matsayin Shugaban Kasa bayan rasuwar dan uwansa, Sheikh Khalifa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50