Mambila: Yadda rikicin fili ke zama na addini da kabilanci

Ga duk wanda ke wajen yankin Mambila da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba, yakan dauki rikicin da ke faruwa a tsakanin al’ummar yankin musamman Fulani da kabilar Mambila da sauran kabilu a matsayin rikici ne na addini ko kabilanci. Sai dai kuma binciken Aminiya ya gano cewa rikicin yana tasowa ne daga rikicin […]

Mambila: Yadda rikicin fili ke zama na addini da kabilanci

Ga duk wanda ke wajen yankin Mambila da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba, yakan dauki rikicin da ke faruwa a tsakanin al’ummar yankin musamman Fulani da kabilar Mambila da sauran kabilu a matsayin rikici ne na addini ko kabilanci. Sai dai kuma binciken Aminiya ya gano cewa rikicin yana tasowa ne daga rikicin fili a tsakanin mutum da mutum, inda har ake zuwa kotuna a yanke hukunci, amma a karshe a dawo ana zubar da jini da asarar dukiya. 

A galibin lokuta ma masu rikicin sun san juna, suna cin kasuwa tare kuma idan za a jingina rikicin da kabilanci, to galibi ba ya da alaka da addini domin kamar yadda bayanai suka nuna akasarin wadanda suke rikicin sukan yi Sallah a masallatai tare kafin su dauki makami su kashe juna.

Kuma wani babban abin da yake da daure kai, shi ne yadda hukumomi da ’yan siyasa da shugabannin jihar suke kasa zakulo masu haddasa rikicin su hukunta su, musamman ganin an san salsalar yadda rikicin ke tasowa da wadanda suke haddasa shi.

Rikici na baya-bayan nan ma kamar sauran wanda ya jawo kai hare-hare a yankunan Yarimaru da Kakara da Leme da suka yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawa tare da asarar dukiyoyi na miliyoyin Naira a makon jiya, Fulanin yankin sun zargi wadansu ’yan kabilar Mambila ne da kai musu hari da misalin karfe 12:00 na ranar Larabar makon jiya saboda takaddama a kan fili.

Fulanin wadanda ga dukan alamu su ne suka fi yin asarar rayuka da dukiya sun zargi ’yan kabilar Mambila da fara kai musu hari, yayin da su ma kabilar Mambila ke zargin Fulanin cewa su suka fara kai musu hari.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a yankin na Mambila ya gano cewa rikicin ya soma ne a kauyen Nyiwa kusa da garin Yarimaru a kan wani fili da wani Bafillace mai suna Jauke Gagarau ya mallaka.

Wakilinmu ya ji cewa ’yan kabilar Mambila sun yi yunkurin karbe filin amma Gagarau ya ki domin a cewarsa yana da takardar mallakar filin. A cewar majiyarmu wannan matsala ta sa Gagarau ya tafi kotu kuma bayan kotu ta binciki maganar ta gano Gagarau ne mai gaskiya sai ta mallaka masa filinsa.  Sai dai bayan kotun ta mallaka wa Gagarau filin ne sai karamar Hukumar Sardauna ta yi watsi da hukuncin kotun ta ce ta bai wa ’yan kabilar Mambila filin, inda su kuma ’yan kabilar Mambila suka kange filin wanda ya hada da wurin da ake bai wa shanu ruwa.

Majiyar ta ce ganin haka ne sai Gagarau da ya samu nasara a kotu a kan filin ya nemi ya kawar da shingen, daga nan ne fada ya kaure a tsakanin ’yan kabilar Mambilla da Fulanin inda nan take aka kashe mutum biyu a kauyen Nyiwa kuma aka ji wa Alhaji Maigari Gagari mummunan rauna tare da wadansu mutane da dama. Majiyar ta ce wannan rikici ya fadada inda ’yan kabilar Mambila suka bazama zuwa dukan kauyukan Fulani suna kai musu hari a cikin dare.

Sai dai wani dan kabilar Mambila mai suna Alhaji Musa Umaru ya shaida wa wakilinmu cewa Fulani ne suka fara harbin matasan Mambila da bindiga a garin na Nyiwa wanda hakan ya tunzura matasansu suka far wa Fulanin.

A wani kauyen Fulani mai suna Kassasa da ke kusa da kamfanin ganyen shayi na Kakara an kashe mutum biyu aka raunata wata tsohuwa mai kimanin shekara 103 kuma sama da mutum 20 suka bace har zuwa hada wannan rahoto ba a ji duriyarsu ba.

Wakilinmu wanda ya ziyarci kauyen ya tarar da mutane na zaman makoki, mata kuma na ta kuka. Kuma ya ga yadda a kauyen aka kone dakuna biyar a wasu gidaje da mota daya kirar Landrober da babura biyu da kayan abinci da sutura.

Wani mazaunin kauyen mai suna Aliyu Bello ya shaida wa wakilinmu cewa suna zaune lafiya da ’yan kabilar Mambila amma sai ga shi sun kawo musu hari sun kashe musu mutane tare da kone gidajensu da ababen hawa da kayan abinci. Ya ce wadanda suka kawo masu hari sun san su, suna cin kasuwa tare da su kuma suna yin Sallah a masalkaci tare.

Aliyu Bello ya shaida wa wakilinmu cewa domin a zauna lafiya su mazauna kauyen Kassasa sun ware wani bangare na filayen gonakinsu sun bai wa ’yan kabilar Mambila amma wannan karamcin bai hana a kai musu farmaki ba.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa matsalar yankin Mambila wadansu ’yan siyasa da ’yan boko daga bangaren kabilar Mambila ne ke zuga ’yan uwansu cewa Fulani sun mallake filaye a yankin kuma dole ne su tashi tsaye su kori Fulani daga yankin su kwace filayensu. Majiyar ta ce mafi yawan ’yan kabilar Mambila mazauna kauyukan tsaunin Mambila ba su da abin hannu, yayin da su kuma Fulani suke da dukiya mai yawa inda hakan ke haifar da hassada a tsakaninsu.

Garin Leme ma matsala ce a kan fili ta haifar da rikici a tsakanin Fulani da kabilar Mambila inda ya jawo kashe Fulani uku, wani mahaifi da ’ya’yansa biyu.

Wakilinmu ya gano cewa wani mai suna Alhaji Magoggo da ke garin Leme ne ya je kotu kan wani fili da mutanen Mambila suka nemi su kwace a hannunsa kuma kotun ta mallaka masa saboda bincike da kotun ta gudanar ta gano cewa yana da takardun malllakar filin

’Yan kwanaki kadan da yanke hukuncin sai wadansu suka biyo dare suka hallaka Alhaji Magoggo, bayan mako daya kuma aka kara biyo dare aka sake kashe ’ya’yan Magoggo biyu.

Jama’ar garin Leme dai suna zargin ’yan kabilar Mambila wadanda Alhaji Magoggo ya yi shari’a da su ne suka kashe Alhaji Magoggo da ’ya’yansa biyu.

A ranar Lahadi kuma sai wutar rikicin ta bulla a garuruwan Yelwa da Maisamari da Tunda inda aka kashe mutane da dama kuma aka kone gidaje masu yawa.

Wannan rikici kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilinmu, ya auku ne bayan da Fulanin suka zargi ’yan kabilar Mambaila da kashe wadansu Fulani mazauna garin na Yelwa su uku a lokacin da suka tafi daji domin su dubo shanunsu.

Hakan a cewar majiyar ta tunzura Fulanin yankin inda suka auka wa garin na Yelwa wanda mafi yawan mazaunansa ’yan kabilar Mambila ne. Baya ga garin na Yelwa wadansu kuma wadanda ake zargin cewa Fulani ne sun kai hari a kauyen Tunga inda suka kone gidaje masu yawa tare da raunata mutane da dama.

Shugabannin kabilar Mambila na zargin cewa Fulanin na kokarin mallake daukacin filayen da suke tsaunin na Mambila ne. Kuma daya daga cikin shugabanin kabilar Mambila, Ambasada Emmanuel Nyiwa ya zargi Fulanin da ke tsaunin na Mambila da cewa sun mallaki manyan bindigogi amma

su kabilar Mambila sanduna da ’yan wukake kawai suke da su domin su masu son zaman lafiya ne. 

A cewar Ambasada Emmanuel Nyiwa, Fulanin ne suka fara kai wa kabilar Mambila hari a rigimar ta baya-bayan nan.

Wani mai magana da yawun al’ummar Fulanin yankin Mambilla, Malam Sale Waziri ya zargi gwamnatin Jihar Taraba da nuna rashin adalci ga al’ummar Fulanin.Ya ce an hallaka Fulani sama da dubu daya tare da kashe shanu fiye da dubu 20, amma har zuwa yau  babu wanda aka kama aka hukunta.

Ya ce kowace kasa a duniya tana amfani da dokoki don tsare rayuka da dukiya, duk kasar da ba ta amfani da dokoki wannan kasar ba za ta zauna lafiya ba, sai ga shi a Jihar Taraba ba a hukunta wadansu mutane saboda adininsu ko kabilarsu.

Lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar a makon jiya ya nuna damuwa kan yadda ake asarar rayuka da dukiya a jihar.

Shugaba kasar wanda ya gana da shugabannin jihar da suka hada da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya a fadar gwamnatin jihar da ke Jalingo, ya ce yawan mutanen da aka kashe a tsaunin Mambila ya fi wadanda aka hallaka a jihohin Benuwai da Zamfara. 

Ya ce ya zo jihar ce domin ta’aziyyar rayukan da aka rasa a rikice-rikicen jihar tare da jajanta asarar dukiyar da aka yi ya ce yana da bayanan dukan abubuwan da suke faruwa a Jihar Taraba.

Shugaba Buhari ya ce akwai bukatar jama’ar jihar su yi nazari mai kyau kan abin da ke faruwa wanda duk wani mai tsoron Allah ya san ba daidai ba ne ya kashe dan uwansa.

Ya ce ya zama tilas a kamo dukan wadanda suke da hannu a kashe-kashen da aka yi a yankin Mambila domin a hukunta su.

Gwamnan Jihar Mista Darius Ishaku ya yi alkawarin cewa zai yi duk abin da ya kamata domin ganin an kawo karshen zubar da jini a jihar. Ya ce zai yi amfani da sarakunan gargajiya domin ganin an samu zaman lafiya tare da bin doka a daukacin sassan jihar.

Ya kuma yaba wa Shugaban kasa kan niyyarsa ta aikin samar da wutar lantarki a madatsar ruwa ta Mambila.

Rikicin na Mambila ya tilasta sanya dokar hana fita a wasu sassa na yankin Mambila a shekarajiya Laraba, bayan da hare-hare suka kara kazanta kwana daya da ziyarar da Shugaban kasa ya kai jihar. Gwamnatin Jihar ta sanya dokar hana fita a Mayo Ndaga ne da ke karamar Hukumar Sardauna.

Yankin na Mambila ya yi fama da rashin zaman lafiya tun daga 1982 inda aka hallaka jama’a masu yawa a wani mummunan fada a tsakanin ’yan kabilar Mambila da na Fanso a 1982 sai kuma fada a tsakanin Fulani da ’yan kabilar Mambilla a shekara 2002, wanda ya kawo sanadiyyar hallaka Fulani sama da 400.

A watan Yunin bara ne aka sake samun wani kazamin fada tsakanin kabilar Mambila da Fulani inda aka kashe Fulani sama da 350 sa’annan aka kashe shanu sama da dubu 20 tare da kona gidajen Fulani sama da 200.