Mambilla: Garin da kowa ke magana da Fulatanci

Mutumin Kaka na magana da Fulatanci da Hausa da Ingilishi.

Mambilla: Garin da kowa ke magana da Fulatanci

Yanke shawarar da hukumomi suka yi a 1940 na ba harshen Fulatanci muhimmanci, shi ya janyo harshen ya watsu sosai a yankin Mambilla a tsakanin al’ummar da akasarinta manoma ne.

“Harshen Fulatanci da waɗanda ba Fulani ba ke magana da shi a wasu garuruwan tsaunin Mambilla musamman yankin Gembu ba gangariya ba ne.

“Karin harshen da ake amfani da shi yanzu ba shi ne wanda ake amfani da shi a da ba. A yanzu harshen ba na asalin ba ne”

Karyayyen Fulatanci

Ana magana da harshen Fulatanci a kusan dukkan garuruwan Mambilla da ba na Fulani ba.

A Taraba Mambilla waje ne da yake da sanyi, duwatsu, gonaki, magangarar ruwa, koguna da sauransu.

A matsayin yanki mai harsuna daban-daban ya sa wurin ya sa aka samu wani Fulatanci karyayye, yanki dai shi ya fi kowane gari sanyi a Nijeriya

Sa’idu Bawa, Shugaban Fulani a Mambilla ya ce, “Idan ka je ainihin garuruwan Fulani za a samu wurin da ake Fulatanci na haƙiƙa.

“Abin da ya janyo aka samu karyayyen Fulatanci shi ne mutanen wurin suna koyon Fulatanci ne yau da gobe don sadarwa a tsakaninsu.

‘Ngare’ da ‘Waru’

Bawa ya ce, “Idan za ka ce mutane su zo a Fulatanci na asali za ka ce musu Ngare amma za a karyayyen Fulatanci za ka ce Waru. Sai dai a yanzu ana amfani da dukkan kalmomin biyu.”

Ya ce ba dukkan Fulani ne ke magana da sauran harsuna kamar harshen Mambilla da Kaka ba.

“Amma za ka iya samun Fulani kaɗan da ke iya yin magana da harsunan yankin.”

Ya ce “Wasu daga cikin Fulani sukan iya magana da harshen Mambilla saboda daɗewa da aka yi ana mu’amala da juna.”

Adamu Yemsa Bafulatani ne da ke zaune a gidan Bawa lokacin da muka tattaunawa, ya ce yana iya magana da Fulatanci da harshen Mambila.

Akwai irinsa da yawa a cikin Fulani da suka jin harsuna da dama, wasu na jingina haka da yawan shan madara da suke yi.

Ode Ekpeme malami ne a Sashen Harshen Ingilishi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya ce idan wasu ƙabilu suka haɗu da wasu, za a iya samun wasu harsuna daga cikinsu.

Yadda harshe na asali zai gudana shi ne keɓaɓɓen ƙauye, a faɗinsa.

Ya ce Gembu inda Bawa ya ce akwai karayayyen Fulatanci shi ne hedikwatar Ƙaramar Hukumar Sardauna da ke Jihar Taraba.

1940

Abubakar Hamma Adama Wakilin Kaka ya ƙara haske kan matsayin Fulatanci a tsakanin al’ummomin tsaunin Mambila.

Ya ce naɗa Ɗan Lawan wanda Bafulatani ne a matsayin hakimi daga Yola a 1940 ya taka rawa a wannan fanni.

Sakaka, Inkiri

Ƙabilar Kaka suna zaune ne a wurare daban-daban a tsaunin Mambila. Wurin da aka fi sani su ne Sakaka da Ndumyaji da Warkaka da Antere da Inkiri.

Wasu suna zaune a Gembu. Yayin da wasu ke zaune a Kamaru musamman ma a yankin Ndong Seh da Fam da Lus da Mbem.

Hakimi

Galadiman Mambilla ya bayyana cewa naɗin da aka yi wa Bafulatani daga Yola a matsayin Hakimi a 1940 shi ne ya janyo suka samu yaɗuwar harshen Fulatanci a Mambilla.

“Bayan ga hakimin da Lamiɗon Adamawa ke naɗawa an kuma naɗa wasu hakiman waɗanda suke Fulani ne.

“Lokacin da suka zo harshensu kaɗai suka iya. Idan za su yi wa wani sarautar mai unguwa a yankinsa, to dole hakimin ya yi magana da harshen ƙauyukan da suke shugabanta

Fulatanci

Hamma’adama ya bayyana cewa “Kafin a naɗa ka a matsayin mai unguwa sai an tabbatar da cewa kana jin harshen Fulatanci.

“Hakan ya sa ya tilasta mutane yin amfani da Fulatanci saboda sauƙin sadarwa a tsakaninsu da hakimin.”

Ya ce, “Mafi yawan shugabannin da aka turo nan kamar ma’aji da jami’an kula da dabbobi da dazuzzuka dukkansu Fulani ne.

“Kasancewar suna shugabantar al’umma ya sa suke magana da harshen Fulatanci da Hausa.

“Wannan ya tilasta mutanenmu su koyi harshen Fulatanci don su samu damar yin magana da shugabanninsu cikin sauƙi.”

Harshen kasuwanci

A cewar Hamma’adama “Ya zama al’ada. Idan ka zo nan ka je kasuwa za ka yi magana da kowa a harshen Fulatanci cikin sauƙi.

“Misali harkar saye da sayarwa ta shanu. Akwai masu sayar da shanu da yawa a yankin. Ana buƙatar shanu da yawa a can musamman a lokacin bukukuwa da sauransu.

Bambancin karin harshe

Umar Zubair shi ne wakilin Mambilla ya ce, “Dalilin da ya sa mutanenmu ke amfani da harshen Fulatanci a matsayin harshen kasuwanci shi ne saboda mu mutanen Mambila muna magana da karin harsuna dabandaban.

“Duk da cewa muna fahimtar junanmu amma dai ba gaba ɗaya ba.”

Ya ce, “Harshen da ake amfani da shi a nan shi ne Fulatanci wannan shi ne harshen kasuwanci.”

Yola

Fulatanci shi ne harshen da ake kasuwanci a tsaunin. “Idan ka je kasuwa za ka sayi wani abu har ka taya to sai dai ka yi magana da Fulatanci.

“Dalili shi ne mutanen da suka fara ziyartar wannan wuri su ne Fulani musamman waɗanda suka zo daga Yola.

“Sai suka zauna a cikin mutanen Mambilla. Idan za su yi sayayya sai dai su yi magana da Fulatanci.

Ya ce “Idan za ka yi magana da su da harshen Mambilla ba za su fahimta ba hakan ya sa ya zame wa mutane dole su koyi Fulatanci har lokacin da ya zama harshen yankin gaba ɗaya.

Makarantar firamare

Zubairu ya taɓo tarihin yadda ya koyi Fulatanci, “A dukkan gidajenmu ba mu yin magana da Fulatanci sai lokacin da aka sanya mu a firamare muka koya a can.

“A yanzu na iya yin Fulatanci. Haka yarana da na kai su makaranta su ma a yanzu sun iya Fulatanci saboda suna mu’amala da sauran ɗalibai ’ya’yan Fulani da Kaka da sauran harsuna daban-daban. Kai hatta Ibo a nan garin suna yin Fulatanci.

Koyon Fulatanci a wata biyu

Onyema Ukwueze ɗan kasuwa ne da ya zo daga Enugu yana zaune ne a Unguwar Kaka ya zauna a Gembu tsawon shekaru, ya ce dukkan ’ya’yansa guda 8 suna magana sosai da Fulatanci.

Ya ce, ya shafe wata biyu yana koyon Fulatanci a Gembu.

Wani ɗan ƙabilar Tibi wanda yake shagon a lokacin ganawa da Mista Ukwueze ya ce shi ma yana iya yin magana da Fulatanci sosai.

Zubairu ya ƙara haske kan yadda ake magana da Fulatanci a gidansa: “Ya danganta da batun da ake tattaunawa.

“A wasu lokuta ina magana da ’ya’yana cikin harshen Fulatanci, su ma su mayar da Fulatancin.

“Fulani ma suna magana da harsunan Mambilla,” in ji shi.

Ɗimbin kare-karen harshe

“Misali ɗan Mambilla daga Kakara ba zai iya fahimtar karin harshen ɗanMambilla daga Gembu ba.

Haka ɗan Mambilla daga Gembu ba zai fahimci na ɗan Mambilla daga Tep ba,” inji Aliyu Mansur Galadiman Mambilla, lokacin da yake magana a kan karkasuwar kare-karen harsunan da ke tsaunin.

Ya bayyana cewa a wasu lokuta abu ne mai ɗaure kai. “Lokacin da Fulani suka zo idan kana son yin magana da ɗan Mambilla daga wani wajen sai dai ka yi masa magana da Fulatanci.

Mutumin Kaka ba ya iya magana da ɗan uwansa ɗan Mambilla ba tare amfani da karin harshensa. Domin ko ya yi ba zai gane ba.

Bunƙasar Fulatanci

Mansur ya bayyana sauran sassan inda ƙabilun yanki suka bambanta, “Mutumin Kaka ba zai iya Magana da ɗan uwansa ɗan Mambilla ba.

Harshen da kawai zai iya magana a fahimta shi ne Fulatanci. Rukunonin mutanen da ke tsaunin Mambilla su fara koyon Fulatanci a hankali har ya zama harshen yankin.

Hatta ɗan Mambilla na Tep da ba zai iya fahimtar ɗan Mambilla daga Gembu ba, ya gwammace ya yi masa Magana da Fulatanci, tunda ba za su fahimci juna ba, wannnan ne ya sa Fulatanci ya mamaye yankin.”

“Mutanen da suka fara haɗuwa da Fulani sun fahimci cewa zai fi kyau su iya Fulatanci.

“A yankunansu suna iya magana da harshensu, amma in aka zo batun sadarwa da Fulani sai su yi da Fulatanci.

Kaka, Panso

“Kaka, Panso, Kembu suk suna magana da Fulatanci. A tsaunin duka waɗannan al’ummomi suna zaune tare. Suna amfani da harshen Fulatanci wanda shi ya haɗa kansu.

“Duk wanda ya koma wurin mutanensa sai ya yi magana da harshensa. Amma idan aka  zo ciniki ko kasuwanci to da harshen Fulatanci ake amfani.

Wannan abu ne da ya zama gama-gari a tsakanin al’ummomin Gembu, Maisamari da Mayon Daga da Nguroje.

Haɗin kai

“Haɗin kai shi ya haifar da harshe ɗaya a cikin al’ummar. Mutumin Panso ko Kaka ba sa fahimtar harshen juna amma suna iya magana da Fulatanci.

“Suna cin abincin Fulani miyar kuka haka kuma su ma suna kiwon shanu.

“A tsaunin idan kai ba a nan aka haife ka ba, to ba za ka iya bambance tsakanin ɗan Mambilla da Bafulatani ko kuma ka bambance mutanen Kaka da Fulani ba.

Arafat Dominic ɗan ƙabilar Panso ne yana ɗaya daga cikin ’yan ƙasa a Gembu, a cewarsa, “Ina magana da harshen Panso da Fulatanci. Ina iya magana sosai da dukkan harsunan biyu. Na koyi Fulatanci a Panso. Iyayena da ’yan uwana duk suna magana da Fulatanci.

A gaskiya Fulatanci shi ne harshen da kowa ke fahimta

Mu 8 muna magana da Fulatanci

Ado Isa manomin masara da wake da doya a koyaushe. Ya ce, “Harshena shi ne Mambila amma ina magana da Fulatanci mun tashi tare da ’ya’yan Fulani.

Ni da ’yan uwana 8 maza uku da mata huɗu duka muna Magana da Mambilla da Fulatanci. Haka suma Fulani suna magana da harshen Kembu da Panso da Kaka.”

Orpah Manasseh Timta ’yar kasuwa ce ta ce ita ’yar Mambilla ce amma tana jin Fulatanci da Ingilishi.

“Ba ma magana da Fulatanci a gida sai dai mun koya a makaranta. Na koya a wajen ’yan ajinmu.”

“Fulani su ne na biyun fara zama a wannan wuri. Mutane suna son yin mu’amala da su saboda alaƙarsu da harkokin kasuwanci.

Kowa na so ya iya magana da Fulatanci saboda ya yi hulɗa da su,” in ji Ahijo Bamanga wanda ya ce an haife shi ne a Gembu.

Fulani suna magana da harsunan Kaka da Mambilla

Hamma’adama ya ƙara da cewa, “Fulani ma suna magana da harsunan Kaka da Mambilla sosai.

A matsayin yaran da suka taso a wannan wuri mutanenmu suna koya musu harshensu su kuma suna koya musu Fulatanci saboda ayyukan mulki da kasuwanci.”

Fahimtar harsuna da dama na da kyau

“Ina ƙarfafa wa mutane gwiwa su koyi harsuna da yawa domin yana taimaka wa mutane su ci gaba da rayuwa.

“Idan na yi magana da abokina da Fulatanci in shi Bafulatani ne ni kuma Mambilla ne, kai kuma Kaka ne wannan na janyo mu fahimci juna.

“Idan har zai zamo muna fahimtar junanmu, ta yaya za a yi mu yi faɗa da juna?

“A gidana muna magana da harsuna biyu, Kaka da Fulatanci. A Mambila kusan kowa na magana da Fulatanci, ‘ in ji Wakilin Jauro.

Kasuwanci Da Banyo

A cewar Napthali Juanboh,wanda manomi ne, “Fulatanci shi ne harshen sadarwa a tsaunin Mambilla. Idan ka je kasuwa ko makaranta za ka tarar shi ne harshen da ake amfani da shi.

“Idan ka yi magana a kan kasuwanci, mutane suna duba ɓangaren Banyo. Kasuwanci ya zo ne ta wancan ɓangare sai Fulatanci ya fara yaɗuwa.”

Ya ƙara da cewa, “Idan muna magana da harsunan juna, to za mu zauna lafiya. Mutumin Kaka na magana da Fulatanci da Hausa da Ingilishi. Muna magana da Fulatanci a gidajenmu.”

Fulatanci ya zama harshen kowa

“Yanayin tsaunin Mambilla na jawo hankalin mutane. Wasu sun taso daga Yola da Jalingo saboda tsananin zafin da ake yi a can.

“Sukan zo su zauna da niyyar idan aka samu sauƙin zafinsu koma,” in ji Zubairu.

Ya ci gaba da cewa “Suna yin haka a lokacin azumin Ramadan. Yin azumin a nan daban yake da yin azumin a sauran wurare kamar Maiduguri da yankunan Adamawa saboda yanayin sanyin wurin mutane suna son wannan wuri sosai.”

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe