Mambobin APC 5 sun rasu a hadarin mota a Kwara

An tabbatar da rasuwar mambobi biyar na jam’iyyar APC a wani mummunan hadari da ya faru kusa da garin Oke zuwa Onigbin a wajen garin Omu-Aran zuwa Ilorin babban birnin jihar ranar Lahadi. Majiyar kamfanin Dillancin Labarai na NAN ta sanar da cewa, hadarin ya auku ne lokacin da mambobin APC tare da wasu masu […]

Mambobin APC 5 sun rasu a hadarin mota a Kwara

Jami’an Hukumar Kiyaye Hatsarin Mota a bakin aiki

An tabbatar da rasuwar mambobi biyar na jam’iyyar APC a wani mummunan hadari da ya faru kusa da garin Oke zuwa Onigbin a wajen garin Omu-Aran zuwa Ilorin babban birnin jihar ranar Lahadi.

Majiyar kamfanin Dillancin Labarai na NAN ta sanar da cewa, hadarin ya auku ne lokacin da mambobin APC tare da wasu masu fada aji na karamar hukumar Irepodun ke hanyarsu na zuwa garin Oro, don murnar gangamin lashe zaben cike gurbi, da dan takarar APC Raheem Olawuyi ya lashe da aka yi ranar Asabar.