Mambobin APC da LP 1,800 sun koma PDP domin goyon bayan Pantami
Matakin yana da nasaba da amincewarsu da ƙwarewa da hangen nesa na Farfesa Pantami wajen jagoranci da ci gaban al’umma.
Aƙalla mambobi 1,800 na jam’iyyun APC da LP a Ƙaramar Hukumar Billiri ta Jihar Gombe sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP domin goyon bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar kuma tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.
An karɓi masu sauya sheƙar ne a hukumance yayin wani taron siyasa da shirin Awareness and Unity Programme ya shirya a garin Billiri.
- Gidauniyar Masarautar Gumel ta buƙaci a faɗaɗa hanyar Maigatari
- Oyebanji ya sake lashe zaɓen gwamnan Ekiti
Daga cikin waɗanda suka fice daga APC zuwa PDP har da tsohon Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, Barrista Aliyu Musa, wanda ya sanar da sauya sheƙarsa tare da ɗaruruwan magoya bayansa.
Da yake jawabi a wajen taron, Musa ya ce matakin da ya ɗauka yana da nasaba ne da amincewarsa da ƙwarewa da hangen nesa na Farfesa Pantami wajen jagoranci da ci gaban al’umma.
Ya bayyana Pantami a matsayin shugaba mai ilimi da gogewa, wanda ke da damar samar da nagartaccen shugabanci tare da hanzarta bunƙasar tattalin arziki da ci gaban Jihar Gombe.
A cewarsa, irin goyon bayan da Pantami ke samu daga mabambantan jam’iyyu da ƙungiyoyin siyasa na nuna yadda al’ummar jihar ke ƙara nuna amincewarsu da shi.
Musa ya kuma yi kira ga al’ummar Billiri da sauran jama’ar jihar da su haɗa kai wajen mara wa wannan buri baya domin tabbatar da ci gaba da shugabanci mai haɗa kan kowa.
Yayin da suke karɓar masu sauya sheƙar, shugabannin PDP a yankin sun yi musu maraba tare da tabbatar musu da cewa za su samu damar gudanar da harkokin siyasa kamar sauran mambobin jam’iyyar.
Sun bayyana sauya sheƙar a matsayin wani gagarumin ci gaba da zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a matakin tushe gabanin zaɓe mai zuwa.
Masu goyon bayan jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun ce shigowar sabbin mambobi daga APC da LP wata alama ce da ke ƙara ƙarfafa goyon bayan da Pantami ke samu a sassa daban-daban na Jihar Gombe.
Taron ya samu halartar jami’an jam’iyya, ƙungiyoyin matasa, shugabannin mata da kuma magoya baya daga gundumomi daban-daban na Ƙaramar Hukumar Billiri.