Mambobinmu har yanzu na sayar da fetur kan N196 –IPMAN
Tuni ‘yan Najeriya suka fara kokawa kan yadda gudajen mai suka tsauwala.
Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta ce mambobinta har yanzu na sayar da man fetur a kan Naira 196 kan kowace lita.
Wannan na zuwa ne biyo bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya sanar a jawabinsa na farko a ranar 29 ga Mayu, 2023.
“Za a kawo karshen tallafin nan da watan Yuni kuma mun yi kokarin sanar da mambobinmu da su ci gaba da siyar da fetur a kan farashin da aka kayyade,” in ji Yakubu Sulaiman, kakakin IPMAN na kasa.
Suleiman ya bayyana haka ne a shirin ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
“Gaskiya duka gidajen man mambobinmu na sayar da fetur a kan farashin da ya dace,” in ji shi.
Suleiman ya ce, farashin da ya dace shi ne “Wasu gidajen mai na siyarwa a kan N195, wasu kuma a kan N196.”
Da yake yin karin haske kan karin kudin mai da gidajen mai suka yi, ya ce bai kamata a ce an yi karin ba duba, da cewar kafin rantsar da sabon shugaban kasa, ana siyar da man a farashin da aka tanadar.
Kakakin na IPMAN, y ace bai kamata ‘yan Najeriya su firgita da cire tallafin ba, domin ba zai fara aiki ba sai a watan Yuli.
Mun baza tawaga don tabbatar da ana siyar da mai a kan farashin da aka kayyade
Suleiman ya ce sun baza tawaga a fadin kasar nan domin tabbatar da farashin Naira 196 kan kowace lita.
Ya ce za su sanya takunkumi tare da rufe duk gidan man da suka samu na siyar da man fetur fiye da kima.
Jawabin Tinubu bayan karbar mulki
Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa a yanzu biyan tallafin man fetur a kasar ya zama tarihi kasancewar ba ya fidda a’i daga rogo.
Tinubu wanda ya bayyana hakan bayan shan rantuswar kama aiki a matsayin Shugaban Najeriya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin ba sabanin yadda gwamnatin da ta gabata ta yi.