Man City da Arsenal sun yi canjaras a Firimiyar Ingila

Yanzu dai ƙungiyar Liverpool ta koma mataki na ɗaya na gasar da maki 67.

Man City da Arsenal sun yi canjaras a Firimiyar Ingila

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester City da Arsenal sun yi kunnen doki a wasan mako na 30 na gasar Firimiyar Ingila.

Man City ta karɓi bakuncin Arsenal da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, sai dai mai masaukin baƙi ba ta samu nasarar doke Arsenal ba.

Hakan na nufin ƙungiyoyin biyu sun raba maki a tsakaninsu.

Yanzu haka ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta koma mataki na ɗaya a gasar da maki 67.

Arsenal kuma ta koma mataki na biyu da maki 65, sai Manchester City mai riƙe da kambun gasar a mataki na uku da maki 64.

Ɗan wasan bayan Manchester City, Natthan Ake ya samu rauni a minti na 26 da fara wasan, yayin da Bukayo Saka na ƙungiyar Arsenal, ya samu rauni a minti na 77.

Yanzu haka dai wasanni tara ne suka rage a kammala gasar Firimiyar Ingila, kuma ana kyautata zaton tsakanin Liverpool, Arsenal da Manchester City wata ƙungiya za ta lashe gasar.

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi