Man. United da Manchester City sun kebe Naira biliyan 348 don sayo Messi da Neymar

Jaridar Sun ta Ingila ta ce kulob din Manchester United da kuma Manchester City da ke Ingila sun fara zawarcin ’yan kwallon FC Barcelona na Sifen  Lionel Messi da Neymar.Rahoton ya nuna kulob din Manchester United da na Man City suna kokarin dauke ’yan wasan ne ko ta halin ka-ka a karshen kakar wasa ta […]

Man. United da Manchester City sun kebe Naira biliyan 348 don sayo Messi da Neymar
Man. United da Manchester City sun kebe Naira biliyan 348 don sayo Messi da Neymar

Jaridar Sun ta Ingila ta ce kulob din Manchester United da kuma Manchester City da ke Ingila sun fara zawarcin ’yan kwallon FC Barcelona na Sifen  Lionel Messi da Neymar.
Rahoton ya nuna kulob din Manchester United da na Man City suna kokarin dauke ’yan wasan ne ko ta halin ka-ka a karshen kakar wasa ta bana.
Rahoton ya ce yayin da kulob din United yake zawarcin  Neymar shi kuwa kulob din City Lionel Messi ne a gabansa.
Kamar yadda jaridar ta sanar, an ce kudin da aka kiyasta kulob din biyu za su kashe wajen cefano ’yan kwallon sun kai Fam biliyan daya, kwatankwacin Naira biliyan 348.
Masana harkar kwallo suna ganin duk da dagewar da kulob din FC Barcelona yake yi na kin sayar da ’yan kwallon a baya, akwai yiwuwar  ya canja shawara wajen cefanar da ’yan kwallon a wannan karo saboda makudan kudin da aka taya su.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa