Manchester City ta sayi Otamandi
Kulob din Manchester City na Ingila ya samun nasarar saye dan kwallon balencia na Sifen Nicolas Otamendi.Rahotannin da suka fito daga jaridun Sifen sun tabbatar kulob din biyu sun cimma matsaya a kan cinikins dan kwallon.Rahoton ya nuna sai da kulob din City ya ajiye Yuro miliyan 45 kwatankwacin Fam miliyan 31 da dubu 700 […]
Kulob din Manchester City na Ingila ya samun nasarar saye dan kwallon balencia na Sifen Nicolas Otamendi.
Rahotannin da suka fito daga jaridun Sifen sun tabbatar kulob din biyu sun cimma matsaya a kan cinikins dan kwallon.
Rahoton ya nuna sai da kulob din City ya ajiye Yuro miliyan 45 kwatankwacin Fam miliyan 31 da dubu 700 kafin su cimma matsaya.
Kulob din United dai ya dade yana zawarcin dan kwallon amma sai ga shi na City ya yi masa zarra inda ya dauke dan kwallon.
Kulob din Manchester City dai da alama zai haskaka a kakar wasa ta bana ganin yadda yake cefano zaratan ’yan kwallo.