Manchester City ta sha kashi a hannun Bournemouth

Wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan wasan Manchester City na fama da rauni.

Manchester City ta sha kashi a hannun Bournemouth

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da ci 2-1, wanda ya kawo ƙarshen wasanni 32 da ta yi ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila.

Antoine Semenyo da Evanilson ne, suka jefa wa Bournemouth ƙwallo a raga, wanda shi ne karon farko da ƙungiyar ta taɓa samun nasara a kan Manchester City.

Bournemouth ta dawo mataki na takwas a gasar Firimiyar Ingila da maki 15.

Wasu daga jiga-jigan ’yan wasan Manchester City na fama da rauni, wanda hakan ya zame mata ƙalubale.

Manchester City na mataki na biyu da maki 23 daga wasanni 10, inda ta yi nasara a wasanni bakwai, ta yi kunnen doki a wasa biyu sai kuma rashin nasara a wasa ɗaya.

Yanzu haka Liverpool ce ke jan ragamar gasar da maki 25 daga wasanni 10 a Firimiyar Ingila.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara