Manchester City ta yanki tikitin wasan karshe na Kofin FA
Riyad Mahrez ne ya zura kwallo uku shi kadai a ragar Sheffield United.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester City ta yanki tikitin kaiwa wasan karshe na cin Kofin FA na Ingila.
Riyad Mahrez ne ya zura kwallo uku shi kadai a ragar Sheffield United a wasan da City suka tashi 3-0 a Wembley ranar Asabar.
- Dalilin da ba za a iya kwaso ’yan Najeriya da suka makale a Sudan ba
- Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 5 a Kano
Wannan ne karon farko da aka zura kwallo uku a zagayen dab da na karshe a gasar FA tun 1958.
’Yan wasan Sheffield United sun yi ta kokarin zura kwallo inda suka samu wata babbar dama ta hannun Iliman Ndiaye wanda ya cilla kwallon da golan City Stefan Ortega ya cafe. Daga nan Mahrez ya samu damar zura kwallo ta farko.
’Yan wasan City sun fuskanci matsaloli a mintunan farko na wasan inda ’yan wasan Paul Heckingbottom suka rika ba su wahala.
Amma daga bisani sun samu dama bayan dan wasan Sheffield Daniel Jebbison ya farmaki Bernardo Silva inda Mahrez ya kara azama ya kara zura kwallo.
Mahrez ya ci kwallo ta uku lokacin da ya kwace kwallon da Jack Grealish ya bugo ta wuce Wes Foderingham a minti na 66.