Manchester City za ta kori ’yan kwallonta takwas

Kulob din Manchester City da ke Ingila ya fara shirin korar takwas daga cikin ’yan kwallonsa a karshen kakar wasa ta bana. Kulob din ya ce zai yi haka ne don ya farfado da martabarsa ganin yadda yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana. Kafar sadarwar Telegraph ta ruwaito cewa daga cikin ’yan kwallon da […]

Manchester City za ta kori ’yan kwallonta takwas
Manchester City za ta kori ’yan kwallonta takwas

Kulob din Manchester City da ke Ingila ya fara shirin korar takwas daga cikin ’yan kwallonsa a karshen kakar wasa ta bana. Kulob din ya ce zai yi haka ne don ya farfado da martabarsa ganin yadda yake tangal-tangal a kakar wasa ta bana.

Kafar sadarwar Telegraph ta ruwaito cewa daga cikin ’yan kwallon da zai raba gari da su akwai Yaya Toure da Samir Nasir da Edin Dzeko da Gaeal Clichy. Sauran sun hada da Aleksander Kolorob da Steben Jobetic yayin da Frank Lampard zai koma Amurka don cigaba da kwallo a kulob din New York City. Shi kuma James Milner kwantaraginsa za ta kare ne a kakar wasa ta bana kuma da alama kulob din ba zai sabunta masa ba.
Daga cikin ’yan kwallon da kulob din ke kokarin sayowa don su maye gurbin wadanda za a sallama akwai Paul Pogba daga kulob din Jubentus na Italiya da Raheem Sterling dan kwallon Liberpool da Kebin De Bruyne da ke kwallo a kulob din Wolfsburg na Jamus da kuma dan kwallon Eberton Ross Barkley.
Rahoton ya ce ana sa ran kulob din zai kashe akalla Fam miliyan 200 kwatankwacin Naira Biliyan 68 da Miliyan 200 wajen cefano sababbin ’yan kwallon.
Kulob din Manchester City dai ya shiga rudu ne bayan ya samu koma baya a bana. A ranar Lahadin da ta wuce ne kulob din Manchester United na Ingila ya yi wa na City kaca-kaca da ci 4-2 a gasar rukunin firimiya ta Ingila, al’amarin da ya sa ya koma na biyar a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar duk da cewa kulob din zakaran kofin a bara.