Manchester United ba ta gama yin cefane ba -Dabid Moyes
A shekaranjiya Laraba ne sabon Kocin Manchester United Mista Dabid Moyes ya fito karara ya nuna cewa har yanzu kulob din bai gama cefanen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a kakar wasa ta bana ba.Wasu na rade-radin tun bayan da kulob din ya sayi dan kwallon baya na kasar Uruguay mai suna […]

A shekaranjiya Laraba ne sabon Kocin Manchester United Mista Dabid Moyes ya fito karara ya nuna cewa har yanzu kulob din bai gama cefanen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a kakar wasa ta bana ba.
Wasu na rade-radin tun bayan da kulob din ya sayi dan kwallon baya na kasar Uruguay mai suna Gullermo barela akwai yiwuwar ba zai sake yin cefana a bana ba.
Wannan rade-radin ne ya janyo hankalin koci Moyes inda ya bayyana cewa shirun da aka ji ba wai ya nuna kulob din ya gama yin cefane ba ne, sai dai ya yi kwanton bauna ne don sayo zaratan ’yan kwallon da kowa zai yi sha’awarsu.
Tuni kulob din Manchester ya nuna sha’awarsa a kan wasu ’yan kwallo da suka hada da mai tsaron baya (Defender) a kulob din Eberton Leighton Baines da dan kwallon FC Barcelona Thiago Alcantara da kuma na Real Madrid Cristiano Ronaldo amma da alama ciniki bai kaya ba.