Manchester United ce ta fi biyan albashi a shekarar 2013 zuwa 2014 a Ingila
Kafar sadarwar wasanni ta Yahoo sports a ranar Litinin da ta wuce ne ta ruwaito kulob din Manchester United da ke Ingila ne ya fi kowane kulob a gasar rukunin firimiya na Ingila biyan zunzurutun albashi a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014. Rahoton ya ce, kulob din ya biya yawan albashin da ya kai […]
Kafar sadarwar wasanni ta Yahoo sports a ranar Litinin da ta wuce ne ta ruwaito kulob din Manchester United da ke Ingila ne ya fi kowane kulob a gasar rukunin firimiya na Ingila biyan zunzurutun albashi a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014.
Rahoton ya ce, kulob din ya biya yawan albashin da ya kai Fam miliyan 214.8 ko Dala miliyan 324 da ya yi daidai da Naira Biliyan 61 da miliyan 800 a bara.
Sai kulob din Manchester City da ya zo na biyu a jadawalin wanda ya biya zunzurutun albashin Fam miliyan 205 kwatankwacin Naira biliyan 60 da miliyan 800 ga ’yan kwallonsa da kuma daukacin ma’aikatan da ke kulob din a shekarar bara. Sai na ukunsu kulob din Chelsea da ya biya albashin Fam miliyan 190 kwatankwacin Naira biliyan 56 da miliyan 430. Sai kulob din Arsenal da ya biya zunzurutun albashin Fam milyuan 166.4 da ya daidai da Naira Biliyan 49 da miliyan 302 a matsayin albashi a kakar wasan da ta wuce.