Manchester United ta fara yunkurin dauke Sergio Ramos daga Real Madrid
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna kulob din Manchester United da ke Ingila ya kusa dauke dan kwallon baya a kulob din Real Madrid na Sifen Sergio Ramos. Kamar yadda wata jarida mai suna AS da ake wallafawa a Madrid ta nuna, Sergio Ramos ya harzuka ne ganin yadda kulob din Madrid ya […]
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna kulob din Manchester United da ke Ingila ya kusa dauke dan kwallon baya a kulob din Real Madrid na Sifen Sergio Ramos.
Kamar yadda wata jarida mai suna AS da ake wallafawa a Madrid ta nuna, Sergio Ramos ya harzuka ne ganin yadda kulob din Madrid ya bar shi cikin duhu na kin sabunta masa kwantaragi. Yanzu saura shekara biyu kenan kwantaragin dan kwallon ta kare. Hakan da wasu dalilai suka sa dan kwallon ya fara tunanin canza sheka.
Idan har cinikin ya kaya, ko shakka babu dan kwallon za su yi musaya kenan da golan Manchester Dabid De Gea da ake ganin zai koma Madrid yayin da shi kuma Ramos zai koma Ingila.
Sannan cinikin zai shiga kundin tarihi a tsakanin kulob din biyu tun bayan wanda ya taba faruwa a tsakaninsu a shekarar 2009 bayan Madrid ta saye Cristiano Ronaldo daga Manchester United.
Sergio Ramos ya koma Madrid ne a shekarar 2005 watau kimanin shekaru 10 da suka gabata, amma a wancan lokaci kulob din ya aza masa farashin Yuro miliyan 200 ga duk kulob din da ake bukatar ya saye shi amma akwai yiwuwar kulob din ya sassauto zuwa Yuro miliyan 65 a yanzu ganin yadda ya fara tsufa kuma babu kofin da bai lashe a kulob din Madrid da kuma a kasar haihuwarsa ta Sifen ba.
dan shekara 29, Ramos a kwanakin baya ne ya nuna bacin ransa a kan korar da aka yi wa tsohon kocin kulob din Madrid Carlos Ancelotti. Sannan ya nuna damuwarsa a kan yadda kulob din ya ki kara masa albashin Yuro miliyan 10 daga Yuro miliyan 6 a shekara da yake karba a halin yanzu. Ya ce bai taba tsammanin kulob din ba zai kara masa albashi bayan ya taimaka wa kulob din lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai a karo na 10 a bara ba, musamman ganin shi ya rama kwallon da Atrletico Madrid ta jefa a ragar Madrid ana saura minti daya a tashi wasan, kuma hakan ya sa Madrid ta farfado kuma ta doke ta Atletico Madrid da ci 4-1 da hakan ya ba ta damar daukar kofin.
Sai dai tuni kulob din Madrid ya karyata rade-radin cewa Ramos zai bar kulob din, inda ya tabbatar da cewa tsakaninsu da dan kwallon mutu-ka-raba ne.