Manchester United ta sallami kocinta, Erik ten Hag

Manchester United ta kori kocin ne biyo bayan gaza kataɓus a ƙungiyar.

Manchester United ta sallami kocinta, Erik ten Hag

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, ta sallami kocinta, Erik ten Hag daga aiki.

Ƙungiyar ta fitar da sanarwa ne a ranar Litinin, inda ta ce matakin zai fara aiki nan take ne.

Wannan dai ya biyo bayan rashin nasara da ƙungiyar ta yi a hannun West Ham United da ci 2 da 1 a ranar Lahadi.

“Erik ten Hag ya rabu da matsayinsa a matsayin mai horas da ’yan wasan Manchester United. Mun gode masa da irin gudunmawar da ya ba mu tsawon lokacin da ya kasance tare da mu sannan muna masa fatan alheri.

“Ruud van Nistelrooy zai riƙe ƙungiyar a matsayin kocin wucin gadi kafin a nemo sabon mai horaswa.”

Rashin ƙoƙarin da ƙungiyar ke yi a kakar wasa ta bana, ya kai ga rasa aikin ten Hag.

Kocin wanda ɗan asalin ƙasar Netherlands ne, ya samu nasarar lashe kofin FA a kakar wasa ta bara.

ten Hag ya shafe tsawon shekara biyu da rabi a ƙungiyar kafin sallamarsa a ranar Litinin.

Yanzu haka Manchester United na mataki na 14 a teburin gasar Firimiyar Ingila, bayan buga wasanni bakwai.

Buni ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki

Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — NBS

Mahara sun kashe mutane 30 a hare-haren Benuwe