Manchester United ta sallami Ruben Amorim

A safiyar Litinin kungiyar ta sanar da sallamar Amorim dan asalin kasar Portugal wanda ya shafe watanni goma sha hudu yana horas da ‘yan wasan.

Manchester United ta sallami Ruben Amorim

Kungiyar Manchester United ta sallami Ruben Amorim daga mukaminsa na mai horas da ’yan wasanta bayan shafe watanni 14 a Old Trafford.

Sallamar ta zo ne jim kadan bayan ya yi kaca-kaca da shugabannin kulob din, tare da nuna rashin jin daɗin goyon bayan da yake samu daga gare su.

Amorim, dan kasar Portugal, ya karɓi ragamar United a watan Nuwamba 2024, inda ya gaji Erik ten Hag.

Sai dai a cikin wasanni 63 da ya jagoranta, ya samu nasara a 24 ne kacal, wato kashi 38 cikin 100 na nasara. Wannan ya sa aka fara tambaya game da dacewar ya ci gaba da zama a kujerar.

A sanarwar da United ta fitar a shafinta na yanar gizo, kulob din ya ce, “Yanzu da da United take matsayi na shida a teburin Gasar Premier, shugabannin kulob din sun yanke shawarar cewa lokaci ya yi da za a yi sauyi.

“Wannan zai ba wa tawagar damar samun matsayi mafi kyau a gasar. Kulob din na godiya ga Ruben bisa gudummawar da ya bayar, tare da yi masa fatan alheri a gaba.”

Maganganun da suka jawo rikici

Kafin a sallame shi, Amorim ya yi jawabi mai zafi bayan wasan da suka tashi 1-1 da Leeds a Elland Road.

Ya ce, “Na zo nan ne in zama manajan Manchester United, ba kawai koci ba. Ban yi murabus ba, zan ci gaba da aikina har sai wani ya zo ya gaje ni.”

Ya kara da cewa, “Idan kulob ba zai iya jure sukar Gary Neville da sauran masu sharhi ba, to akwai bukatar a sake tsarin kulob din. Akwai sashen binciken ’yan wasa, akwai daraktan wasanni, kowa ya yi aikinsa. Na zo nan in zama manaja, ba kawai koci ba.”

Ana ganin wannan jawabi mai zafi da kuma sakamakon wasanni da bai burge ba, suka sa Amorim ya rasa aikinsa a Old Trafford.

Yanzu dai United ta riga ta nada tsohon ɗan wasa Darren Fletcher a matsayin mai rikon kwarya kafin a samo sabon mai horaswa na dindindin.