Manchester United za ta maye gurbin Luis ban Gaal?
Wata jarida mai suna La Republica a shekaranjiya Laraba ne ta ruwaito cewa kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara yunkurin maye gurbin kocinsa Luis ban Gaal da kocin Jubentus na Italiya Massimiliano Allegri a karshen kakar wasa ta bana.Rahoton ya ce mahukunta Manchester suna sha’awar yadda kocin Jubentus na Italiya din yake […]
Wata jarida mai suna La Republica a shekaranjiya Laraba ne ta ruwaito cewa kulob din Manchester United da ke Ingila ya fara yunkurin maye gurbin kocinsa Luis ban Gaal da kocin Jubentus na Italiya Massimiliano Allegri a karshen kakar wasa ta bana.
Rahoton ya ce mahukunta Manchester suna sha’awar yadda kocin Jubentus na Italiya din yake tafiyar da aikinsa ne musamman ganin yadda ya yi kokari a kakar wasan da ta wuce.  Kocin dai ya samu nasarar lashe wa Jubentus manyan kofun biyu na Italiya a kakar wasan da ta wuce sannan ya samu nasarar kai kulob din wasan karshe a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a bana.
A shekarar 2014 ne Luis ban Gaal ya sanya wa kulob din Manchester United hannu a kwantaragin shekara biyu amma  akwai yiwuwar ya raba gari da United kafin kwantaraginsa ta kare.