Mandela ya bar kadarorin Dala miliyan hudu da dubu 100
Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela ya bar gadon Dala miliyan hudu da dubu 100 ga iyalansa da ma’aikatansa da makarantu da jam’iyyar ANC mai mulki, kamar yadda aka samu a rubuce cikin wasiyyarsa.Mataimakin Shugaban Kotun Tsarin Mulki, Dikgang Moseneke ya bayyana cewa, da farko a kimanta darajar gadon da kudin Rand miliyan 46, […]

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu, Nelson Mandela ya bar gadon Dala miliyan hudu da dubu 100 ga iyalansa da ma’aikatansa da makarantu da jam’iyyar ANC mai mulki, kamar yadda aka samu a rubuce cikin wasiyyarsa.
Mataimakin Shugaban Kotun Tsarin Mulki, Dikgang Moseneke ya bayyana cewa, da farko a kimanta darajar gadon da kudin Rand miliyan 46, wanda ya yi daidai da Dala miliyan hudu da dubu 100. An kuma karanta wa iyalan Mandela abin da ke kunsh a wasiyarsa.
Moseneke ya bayyana wa manema labarai cewa, matar Mandela ta uku, Graca Machel, za ta hakura da bukatarta na kwasar rabin dukiyar da marigayin ya bari, inda za ta bukaci a danka mata wasu kadarorin da suke kasarta ta haihuwa, wato Mozambikue. Kuma Nelson Mandela da ke yada akidunsa, ta zuba bayanai game da wannan wasiya ta Mandela.