Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina

Mutane da dama sun bayyana yadda aikin idon kyauta ya ceci rayuwarsu.

Mangal ya bayar da tallafin N257m don yi wa marasa galihu aikin ido kyauta a Katsina

Fitaccen attajirin nan Alhaji Dahiru Mangal, ya ɗauki nauyin yi wa marasa galihu a Jihar Katsina aikin ido kyauta, inda ɗaruruwan mutane ke samun kulawar likitoci ba tare da biyan ko sisi ba.

A yayin da wakilin Aminiya, ya ziyarci Asibitin Ido da ke birnin Katsina, marasa lafiya da dama da suka ci gajiyar aikin sun bayyana farin cikinsu da godiya kan tallafin na sama da Naira miliyan 257.

Malama Indo, wadda ta fito daga garin Dankama da ke Ƙaramar Hukumar Kaita, ta bayyana farin cikinta da samun tallafin.

Ta ce: “Na kwashe kusan shekara guda ina fama da ciwon ido. Da zarar yamma ta fara yi, sai na kasa fitowa saboda duhu. Amma yanzu ina gani lafiya lau, babu wata matsala.

“Mun kwana uku a nan asibiti, ba mu rasa komai ba, har abinci ake ba mu. Wallahi ba zan iya cewa na kashe komai ba sai kuɗin mota kawai.

“Muna roƙon Allah Ya saka wa wanda ya ɗauki nauyin wannan aiki da alheri,” in ji ta.

Shi ma wani dattijo mai suna Malam Khalha Jibiya, ya bayyana jin daɗinsa game da aikin.

Ya ce an masa aiki, an kuma ba shi tabarau, sannan yanzu yana gani ba tare da wata matsala ba.

“Idan waɗanda Allah Ya hore musu dukiya za su riƙa taimaka wa gajiyayyu kamar haka, da matsalolinmu da dama sun ragu.

“Muna addu’a Allah Ya saka wa mai ɗaukar nauyin wannan shiri da alheri.” inji Malam Khalha.

Dukkanin marasa lafiyan da Aminiya ta zanta da su, sun yi godiya, musamman ganin cewa aikin ido da magungunan da ake ba su kyauta ne baki ɗaya.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki