Manhajar fina-finan Indiya da Harshen Hausa za ta soma aiki

Sai dai hakan wasu na gani wannan ci gaban mai hakar rijiya ne da zai kashe al’adar Hausawa.

Manhajar fina-finan Indiya da Harshen Hausa za ta soma aiki

Wayar Salula

Fina-finan Indiya wadanda aka fassara su zuwa Harshen Hausa sun samu tagomashi da kaddamar da wata manhaja ta kallon fina-finan zalla.

Manhajar mai suna Kallo.com za ta farar aiki ne cikin watan Oktoba, a cewar Maijidda Modibbo wacce ta kirkiri manhajar a hirarta da wakilinmu a ranar Talata.

Maijidda ta ce manhajar za ta kawo wa masu kallo fina-finan Indiya da dumi-duminsu cikin Harshen Hausa wanda hakan zai burge Hausawa masoya fina-finan na Indiya da ke ciki da kuma wajen kasar.

Sannan ta kara da cewa, da akwai kamanceceniya mai yawa tsakanin wasu al’adu na Hausawa da na Indiya, wanda hakan ta sa finafinan Indiyan ke da farin jini.

A ‘yan shekarun nan an samu karuwar yawan fina-finan Indiya da ake fassarawa zuwa Harshen Hausa, wadanda wasu kamfanonin fassara suke yi, da kuma yadawa ta hanyar masu tura wa mutane a wayoyin hannu.

Wasu gidajen talabijin na ciki da wajen kasar su ma sun samar da irin wadannan fina-finan da fassarar Hausa wadanda suka kara kawo musu farin jini.

Sai dai hakan wasu na gani cewa wannan cigaban mai hakar rijiya ne, domin a ra’ayinsu, wadannan finafinai babu abin da za su amfanawa harshen Hausa da illa kashe al’ada.